Yadda Facebook ya tona asirin mai kisa

Cheyenne Antoine a hagu tare da wadda ta kashe Brittney Gargol. Hakkin mallakar hoto Facebook
Image caption Ana iya ganin damarar da Cheyenne Antoine ta saka a jikinta a hoton da suka dauka da wadda ta kashe Brittney Gargol

An gurfanar da wata mata 'yar kasar Canada gaban kuliya bisa kashe kawarta bayan da 'yan sanda suka gano makamin da aka yi amfani da shi wajen kisan a cikin daya daga cikin hotunan da aka dauka kuma aka yada a kafar Facebook.

Cheyenne Rose Antoine, mai kimanin shekara 21, ta amsa laifin kashe Brittney Gargol a ranar 18 ga watan Maris din 2015.

An samu gawar a kusa da wata bola da ke Saskatoon hade da damarar Antoine a kusa da gawarta.

An dai yankewa Antoine, hukuncin zaman gidan kaso na tsawon shekara bakwai.

An gano ita ta yi kisan bayan da ta sanya wani hoto da suka dauka da marigayiyar ta sanya shi a shafinta na Facebook, kuma a hoton an nunata sanye da damarar da aka gano a kusa da gawar.

'Yan sanda sun ce babu wata shaida da aka gano wadda ta tabbatar da labarin kanzon kuregen da Antoine ta bayar da farko inda ta ce sun je wata mashaya ne tare bayan an yi wata walima a gida, daga nan ne sai Gargol ta fita da wani mutum da ba ta san shi ba.

'Yan sandan sun ce sun ga hoton Antonie sanye da damarar a shafin Facebook na Gargol.

Yanzu haka dai Antonie ta amsa cewa ita ta shake kawarta Gargol, kuma ta yi hakan ne bayan sun bugu da barasa sai musu ya kaure a tsakaninsu.

Shin ko Antoine ta yi nadama?

Kwarai da gaske, shi ya sa ma alkalin ya amince da hukuncin zaman gidan kaso na tsawon shekara bakwai ga Antoine bayan da aka same ta da laifi.

Antoine ta yi nadama tana mai cewa" Ba zan taba yafe wa kai na ba. Ba bu wani abu da zai dawo mini da aminiyata. Ina mai matukar nadama da bada hakuri, kuma hakan ba zai kara faruwa ba", Wannan shi ne abin da Antonie ta fada.

Ko me iyalan Gargol ke cewa?

Kafin a yankewa Antoine hukunci, sai da goggon Gargol, Jennifer Gargol, ta bayar da bahasi a kotu game da wadda aka kashen.

Goggon Gargol ta ce " Ba zamu taba daina tunawa da Brittney ba da kuma abin da ya faru a wannan dare".

A wajen kotun kuwa, kawun marigayiyar ne ke bayyanata da cewa yarinyar kirki ce wadda ba ta cancanci a yi mata wannan kisa ba.

Labarai masu alaka

Karin bayani