Nigeria: Zazzabin Lassa ya sa an rufe makaranta

lassa Hakkin mallakar hoto SPL

An bayar da umarnin a rufe wata makaranta tsawon mako guda a jihar Ebonyi da ke kudu maso gabashin Najeriya saboda bullar cutar zazzabin Lassa da aka samu.

Baya ga rufe makarantar har zuwa ranar 26 ga watan da muke ciki, wani jami'in kiwon lafiya a jihar ya tabbatar wa BBC cewar, an gano mutum 130 da suka yi mu'amala da wadanda suka kamu da cutar kokuma cutar ta kashe su.

Jami'in dai ya ce a halin yanzu ana kan yi wa mutum hudu da suka kamu da cutar magani, yayin da aka kebe wasu mutane shida domin ana fargabar sun kamu da cutar.

A halin yanzu dai ana gwaje-gwajen jinin mutum 21 da ake ganin sun kamu da cutar.

Wadannan matakan dai sun biyo bayan mutuwar wasu likitoci biyu da jami'an jinya sakamakon kamuwa da cutar.

Alamomin cutar ta zazzabin Lassa sun hadar da zazzabi da yawan gajiya da tashin zuciya da amai da gudawa da ciwon kai da ciwon ciki da fitowar kuraje a makogwaro da kuma kumburin fuska.

Kwayar cutar na yaduwa ne ga mutanen da suka ci bera da ke dauke da cutar ko kuma cin abincin da bera ya yi fistari a ciki.

Kazalika za a iya kamu wa da cutar ta hanyar haduwar jini ga wanda ke da cutar.

Labarai masu alaka