Everton ta karbo Walcott daga Arsenal

Walcott, mai shekara 28, shi ne na biyu da kungiyar ta saya a kasuwar sayen yan wasa da aka bude a watan Janairu Hakkin mallakar hoto Catherine Ivill
Image caption Walcott, mai shekara 28, shi ne na biyu da Everton ta saya a kasuwar da aka bude a watan Janairu

Everton ta kammala daukar dan kwallon Arsenal Theo Walcott bisa yarjejeniyar shekara uku da rabi a kan kudi sama da fam miliyan 20.

Walcott, mai shekara 28, shi ne na biyu da kungiyar ta saya a kasuwar cinikin 'yan wasa da aka bude a watan Janairu bayan daukar Cenk Tosun daga Besiktas akan kudi fam miliyan 27.

Sayen dan kwallon ya kawo karshen shekara 12 da ya shafe a Arsenal, inda ya ci kwallaye 108 a wasa 397 da ya buga.

Walcott wanda Arsene Wenger bai taba fara wasa da shi ba a kakar bana, ya yi amannar cewa Allardyce zai taimaka ma sa.

"Ina jin cewa lokaci ne ya yi da zan bar Arsenal", In ji dan wasan.

Ya kara da cewa,"Abin bakin ciki ne amma kuma abun farin ciki ne a lokaci daya, kuma ina son na ciyar da aikina gaba kuma na taimaka wa Everton samun nasara kamar yadda suka samu a baya.

A wata sanarwa, Arsenal ta ce"Dukkanmu muna godiya ga Theo bisa gudunmawar da ya ba wa kungiyar, kuma muna yi masa fatan alkhairi".

Kocin Arsenal Arsene Wenger ya tabbatar da cewa ba ya son Walcott ya bar kungiyar.

Labarai masu alaka