Kotu ta tabbatar da 'yan IPOB a matsayin 'yan ta'adda

Kotu ta tabbatar da IPOB a matsayin 'yan ta'adda Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kotu ta ci tarar kungiyar IPOB kudi N500,000.

Babbar kotu a Abuja ta tabbatar da kungiyar IPOB da ke fafutikar kafa kasar Biafra a matsayin ta 'yan ta'adda bayan ta yi watsi da koken da kungiyar ta shigar.

Kotun dai ta tabbatar da hukuncin farko ne da ta yanke a watan Satumban da ya gabata bayan ayyana IPOB a matsayin kungiyar 'yan ta'adda.

Bayan hukuncin ne mambobin kungiyar suka tunkari kotun domin ta wanke su a matsayin 'yan ta'adda.

Yanzu kuma kotun ta yi watsi ne da kalubalantar matakin da lauyan kungiyar ya shigar inda ya ce IPOB kungiya ce ta kasashen waje da ba ta da rijista a Najeriya.

Alkalin babbar Kotun Mai shari'a Abdu Kafarari wanda ya yi watsi da koken kungiyar, ya ce ana iya kama mamban wata kungiya ta kasashen waje idan har an same shi da laifi a wata kasa.

Har ila yau, Alkalin ya ce ba wani hakkinsu da aka keta, kamar yadda lauyan da ke kare kungiyar Ifeanyi Ejiofor ya gabatar.

Alkalin kuma ya ci tarar kungiyar ta IPOB kudi N500,000.

Rundunar sojin Najeriya ce dai ta ayyana kungiyar IPOB a matsayin ta ta'addanci, ko da yake daga baya rundunar sojin ta sauya matsayin, inda ta kira IPOB barazanar tsaro ga kasa.

A lokacin kuma 'yan kungiyar da ke fafutikar kafa kasar ta Biafra sun fito sun ce su ba 'yan ta'adda ba ne.

Labarai masu alaka