An dakatar da 'Principal' saboda zane dalibai a Nigeria

An dakatar da 'Principal' saboda zane dalibai Hakkin mallakar hoto NASARAWA STATE
Image caption Ma'aikatar ilimi a jihar Nasarawa ta haramta dukan dalibai

An dakatar da wani shugaban makaranta da ke jihar Nasarawa a Najeriya, bayan da aka sanya wani hoton bidiyo da aka yada bidiyonsa a shafukan sada zumunta yana yi wa wasu dalibai dukan tsiya.

Kwamishinan ilimi na jihar Tijjani Ahmed, ya ce an dakatar da shugaban makarantar tare da wasu abokan aikinsa na tsawon wata guda kuma tuni aka kaddamar da bincike a kan lamarin.

A cikin hoton bidiyon, an nuna yadda malamin ya daddage yana dukan wasu dalibai da bulala a makarantar GSS Nasarawa Eggon.

Hoton bidiyon dai ya mamaye kafofin sadarwa na intanet.

Kwamishinan ya ce, tuni aka haramta aikata irin wannan hukuncin a daukacin makaratun jihar.

Sannan ya ce duk malamin da aka samu da aikata irin wannan laifi za a ladabtar da shi.

Kwamishinan ya kara da cewa za a iya ladabtar da dalibai ta hanyoyi da dama ba lalle sai an dauki irin wannan mataki mai tsauri na yi wa dalibai dukan kawo wuka.

Labarai masu alaka