An hana bakar ba'amurkiya zuwa sararin samaniya

Dr Jeanette Epps Hakkin mallakar hoto NASA

An cire wata ba'amurkiya bakar fata Jeanette Epps, da ta samu horo a bangaren ilimin sararin samaniya daga cikin wadan da zasu shiga sararin samaniya watanni kadan kafin tafiyar.

Dr Epps, ita ce bakar fatar Amurka ta farko da ta samu shiga cikin wadanda zasu yi tafiyar.

A watan Yuni ne aka shirya za ta shiga cikin 'yan sama jannati, amma sai aka maye gurbinta da wata.

Har yanzu Hukumar Kula da sararin samaniya ta Amurka NASA, ba ta bayar da dalilin da ya sa aka cireta ba, sai dai ta ce za ta tara a gaba.

An haifi Jeanette Epps a Syracuse, ta kuma kammala karatun digiri na biyu a bangaren hada injinan jirgin sama a 2000.

Bayan ta kammala karatun ta yi aiki a fannin gwaje-gwaje na tsawon shekara biyu, kafin hukumar CIA ta dauketa aiki.

Hakkin mallakar hoto NASA
Image caption Syracuse ke nan, wacce a da aka shirya za ta tafi sararin samaniya a watan Yuni.
Hakkin mallakar hoto NASA
Image caption Za a maye gurbin Dr Epps will da Serena Auñón-Chancellor, wacce ta yi aiki da jami'an cibiyar sararin samaniya a Rasha.

A wata tattaunawa da aka yi da ita a mujallar Elle bara, Dr Epps ta ce," Na yi matukar farin ciki a lokacin da nake tunanin kasancewa a sararin samaniya, saboda ina kawatanta tafiyar da ta zuwa filin daga".

Ta kara da cewa ,"lokacin da mutane suka dawo daga sararin samaniya, naga yadda suke zumudin su kara komawa".

Har yanzu NASA, ba ta bayar da dalilin da ya sa aka cireta daga tafiyar ba.

Wacce aka maye gurbinta mai suna Serena Aunon-Chancellor wata likita ce daga Fort Colins, a jihar Colarado.

A baya Dr Aunon-Chancellor ta shafe sama da wata tara tana aiki da jami'an sararin samaniya a kasar Rasha.