Kudin cizo ya addabi fasinjan jirgi

British Airways Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kudin cizo ya addabi fasinjan jirgin British Airways

Hukumar sufurin jiragen sama a Ghana ta yi gargadin daukar mataki a kan kamfanin jirgin saman Birtaniya wato British Airways saboda kudin cizo a wasu jiragen kamfanin.

Ministar sufurin jiragen sama a kasar Cecelia Dapaah ta ce kamfanin na iya fuskantar takunkumi idan har bai dauki mataki ba a kan kudin cizo da aka ruwaito sun dabaibaye wasu jiragensa da ke jigila zuwa kasar.

Rahotanni daga Birtaniya sun ce kudin cizon da aka gani yana yawo a daya daga cikin jiragen na British Airways ya tilasta an dakatar da jirgin a tashar Heathrow a London.

British Airways dai bai musanta kudin cizon ba kuma ya ce an canza jirgin wanda ya kamata ya tashi zuwa Accra, a wani sakon imel da kamfanin ya turawa BBC.

Kmfanin ya ce wannan matsala ce da ba kasafai ake samu ba, kuma jami'ansa na kokarin magance matsalar.

Jirgin sama ya yi karo da tsuntsu a Burundi

Anya za mu iya kawar da kudin cizo?

British Airways ya shafe shekaru 80 yana jigila daga Birtaniya zuwa Ghana, amma ana ganin matalar kudin cizon na iya rage wa kamfanin yawan kwastamomi.

Kudin cizon dai wani karamin kwaro ne da ke shan jinin mutane, kuma yawanci ya fi makalewa ne a jikin gado da gefen katifa.

Sannan ya fi yaduwa a tufafin mutane a wurare na haduwar jama'a kamar Otel da jiragen sama.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kudin Cizo na rayuwa ne da jinin mutane

Labarai masu alaka