Celine Dookhran: An fada ma ta saura 'minti 10 ta mutu'

Celine Dookhran Hakkin mallakar hoto Twitter
Image caption Celine Dookhran was found dead in an empty house in Kingston Upon Thames

Wata mata wadda ta tsira da ranta a hannun wani wanda ta ce ya yi mata fyade ta bayyana wa kotu halin da ta samu kanta a lokacin da lamarin ya auku.

Matar da ba za a iya bayyana sunanta ba saboda dalilan shari'a ta fada wa kotu cewa Mujahid Arshi mai shekara 33 ya yi mata fyade, sannan daga baya ya yanka wuyanta da hannayenta da wuka kafin ya sanar da ita cewa sauranta minti 10 ta mutu.

Ana tuhumar Mista Arshid da laifin yi wa wata mata mai suna Celine Dookran mai shekara 20 fyade da kuma laifin kashe ta.

Ya karyata dukkan tuhume-tuhumen da akai masa.

An gano gawar Ms Dookran a cikin wani firji babba a watan Yulin 2017 a wani gida da babu kowa cikinsa a yankin Kingston dake kudancin birnin Landan.

A rana ta uku da fara shari'ar, an nuna wa alkalin kotun wani bidiyo da wannan matar da ta tsira da ranta ta bayyana wa 'yan sanda masu bincike abin da ya faru da ita kwana biyu bayan harin.

Hakkin mallakar hoto UNKNOWN
Image caption Mujahid Arshid (hagu) da Vincent Tappu na fuskantar tuhumar yin garkuwa da matan biyu da kisan Ms Dookran

Labarai masu alaka