'Jigawa ta dauki malaman makaranta 330'

Gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar
Image caption Gwamnan jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar

Gwamnatin jihar Jigawa, ta dauki malaman makarantar babbar sakandire 330, wadanda suka kammala karatun digiri.

Malaman makarantar sun hada da maza da mata da suka kammala karatun digiri.

Mai magana da yawun ofishin shugaban ma'aikatan jihar, Isma'il Ibrahim Dutse, ya sanar da haka a ranar Jumma'a.

Da ya ke mika wa sabbin ma'aikatan takardar daukar aikin ranar Alhamis, Alhaji Muhammad Inuwa, ya bayyana cewa, ma'aikatan zasu koyar a fannin Turancin , da lissafi, da kuma sauran darussan kimiyya a makarantun da za a turasu da ke sassan jihar.

Shugaban ma'aikatan ya ce,"Wannan wani bangare ne daga aikin gwamnatin mai ci a kokarin da take na cike gibin da ake da shi a bangaren ilimi."

Kwamishinar ilimin jihar Hajiya Rabi Ishaq, ta ce,"Wannan ne karon farko da gwamnatin jihar ta dauki malaman makaranta sama da 300 a karkashin ma'aikatar".

Labarai masu alaka