Afirka a makon nan cikin hotuna

Zababbun hotunan al'amuran da suka faru a Afrika da kewaye a makon nan

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasu mutane na zaune a kusa da zanen fitaccen dan kwallon Liverpool Mohamed Salah a kofar shagon sayer da shayi a Al-kahira babban birnin Masar
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wani dan Somaliya na nuna kwarewarsa a fagen tamaula a gabar tekun Lido da ke babban birnin kasar Mogadishu.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu yaran Somaliya na buga kwallo a gabar tekun Lido a Mogadishu.
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wannan yaron dan Masar hankalinsa ba a kan kwallon kafa yake ba, domin kuwa shi ya dukufa ne yana yin zikiri na mabiya darikar Sufaye.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wata mata 'yar Sudan ta yi ado da kayan gargajiya a Madrid babban birnin Spaniya.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wani yaro ya rufe bakinsa lokacin da yake wucewa ta wurin da masu zanga-zanga suke kona taya a Lusaka babban birnin Zambia.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yaran Afirka ta Kudu na murnar bikin cika shekara 106 da kafa jam'iyyar ANC a kasar.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kabilar Khoisan ma sun yi murnar cika shekara 106 da kafa jam'iyyar ANC
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kabilar Berbers da ke Arewacin Afirka na murnar sabuwar shekararsu a Ath Mendes da ke gabashin babban birnin Algeria.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wani mutum ya saka tutar Berber ya hau doki don ci gaba da wasannin murnar sabuwar shekarar Yennayer.
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wasu 'yan Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo na yin rawa da waka don nuna alhininsu a kan cika shekara 17 da kashe tsohon shugaban kasar kuma mahaifin shugaban kasar na yanzu Laurent Kabila, a babban birnin kasar Kinshasa.

Labarai masu alaka

Labaran BBC