Kabul: An kawo karshen harin Otel din Intercontinental

A man tries to escape from a balcony at Kabul's Intercontinental Hotel during an attack by gunmen in Kabul, 21 January Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mutane da harin ya rutsa da su a otel din sun rika daura zanen gado domin tserewa daga benen.

Wani mummunan hari da wasu 'yan bindiga suka kai akan otel din Intercontinental dake birnin Kabul ya zo karshe, inji jami'an tsaro a birnin.

Ma'aikatar tsaron kasar ta sanar da cewa a kalla faraen hula biyar sun rasa rayukansu a otel din, har da maharan su uku

An dai ceto mutum fiye da 150 bayan da dakarun kasar Afghanistan suka yi wa otel din kawanya tun cikin dare domin su fitar da maharan.

Masu nazarin al'amuran tsaro na ganin cewa an yi sakaci da aka bar maharan dauke da manyan makamai iya shiga wannan wuri dake da matakan tsaro sosai.

A halin da ake ciki, babu wata kungiya da ta dauki alhakin wannan harin na baya-bayan nan, amma ana ganin ba zai wuce kungiyar Taliban ba wacce ta taba kai wa otel din hari a 2011.

Wadanda aka ceto din sun hada da 'yan kasar waje 41.

Hukumomin kasar sun ce maharan su hudu ne suka kai harin, amma daga baya sun sanra da cewa uku ne.

A kalla 'yan bindiga su hudu ne suka kai harin kan Otel din Intercontinental, inji jami'an kasar Afghanistan.

Dakarun sojin na kundunbala sun sai nasarar kashe biyu daga cikin maharan, kamar yadda kakakin ma'aikatar harkokin cikin gida ya sanar. Ya ce ana can ana neman sauran.

Maharan sun fad cikin otel din ne dauke da makamai, inda suka rika harbin baki da kuma ta da nakiyoyi.

A kala mutum biyar sun sami rauni, kamr yadda jami'ai ke cewa. Amma babu adadin wadanda suka rasa rayukansu.

Harin ya fara ne daga misalin karfe 9 na dare, kuma wasu rahotanni na cewa 'yan bindigan sun rika harbin masu gadin otel din a yayin da suke kokarin kutsawa cikin otel din mai hawa biyar.

Wani mazaunin otel din ya fada wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa mutane sun boye a cikin dakunansu.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kabul Otel din Intercontinental yana cikin manyan gine-ginen birnin Kabul

Wani jami'in ma'aikatar tsaro sun fada wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa an fara binciken yadda maharan suka iya shiga otel din bayan da aka mika tsaron otel din ga wani kamfani mai zaman kansa mako biyu da suka gabata.

Ya ce, "Da alama sun bi ta wata kofar baya ce ta bangaren masu girki."

Labarai masu alaka