Za a gudanar da zanga-zanga a Congo

Shugaba Kabila dai na ci gaba da mulki a kasar duk da wa'adinsa ya cika bisa tsarin mulkin kasar
Image caption Shugaba Kabila dai na ci gaba da mulki a kasar duk da wa'adinsa ya cika bisa tsarin mulkin kasar

A yau ne za a gudanar da wata zanga-zanga wadda ba a bada izinin yin ta ba, ta nuna kin jinin gwamnatin Shugaban Congo Joseph Kabila a babban birnin kasar Kinshasa.

Cocin roman katolika mai fada a ji a Jamhuriyar demokradiyyar Congo ne ya yi kira da a fito zanga-zangar, inda ya soki jami'an tsaro a kan tarwatsa wata zanga-zangar kin jinin gwamnatin da a ka yi ran jajiberin sabuwar shekara inda har mutane 5 su ka rasa rayukansu.

An yi kira ga mabiya cocin roman katolika da su fito bayan taron ibada a yau lahadi domin yin zanga-zangar lumana.

Shugaba Kabila dai na ci gaba da mulki a kasar duk da wa'adinsa ya cika bisa tsarin mulkin kasar da kuma yarjejeniya da ya yi da cocin katolikan.

Kisan kiyashin Congo: 'Sai mun taka gawawwaki mu tsere'

Jami'an tsaro sun kashe 'yan gudun hijira 30 a Congo

Labarai masu alaka