Ya kamata a rika wa mata 'Gwajin Angelina Jolie'

Angelina Jolie Hakkin mallakar hoto Getty Images

Likitoci sun ce gwajin cutar daji wato kansa ga mata, har da wadanda ba su da hatsarin kamuwa da cutar hanya ce mai kyau a kokarin rage mace-mace da ake yi daga cutar.

An cire wa fitacciyar 'yar fim Angelina Jolie nononta da wasu bangarori na mahaifarta saboda ta na cikin masu matukar hatsarin kamuwa da cutar ta daji.

Yawanci akan nemi mata su yi gwaji ne kawai idan an tabbatar akwai masu cutar a cikin iyalin gidan da ta fito.

Amma wasu likitoci a asibitin Jami'ar Queen Mary dake birnin Landan sun ce akwai alfanu idan aka fara gwada kowa.

Idan aka gane mace na dauke da kwayoyin halittar cutar ta daji, ana iya daukan matakin yi mata tiyata domin cire bangaren da ya fi hatsarin kamuwa da cutar kamar yadda aka yi wa Angelina Jolie.

An wallafa wannan rahoton ne a wata mujalla ta cibiyar kula da cutar daji, wato National Cancer Institute.

Bibiyar na ganin akwai tasirin yi wa matan da shekarunsu na haihuwa suka wuce 30 su fiye da miliyan 27 wannan gwajin a Birtaniya.

Likitocin sun lissafa amfanin gwajin:

  • Zai yi rigakafin kamuwa da cutar kansa ta nono kimanin 64,500
  • Zai zama rigakafi ga wadanda za su iya kamuwa da cutar kansa ta mahaifa su 17,500
  • Gwajin zai kuma ceto rayukan mata fiye da 12,300

Labarai masu alaka