Ko za ka iya cudanya da tubabben dan Boko Haram?

Boko Haram Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption 'Yan Boko Haram da aka suka tuba za su yi cudanya a jama'a

A yayin da rundunar sojin Najeriya ta ce ta sauya dabi'un wasu 'yan Boko Haram tare da sakin su don su saje cikin al'umma, wasu 'yan Najeriya na ganin matakin ya dace yayin da wasu ke ganin cudanyarsu da jama'a abin fargaba ne.

Da dadewa ne dai gwamnatin Najeriya ta bude kofar tuba ga 'yan Boko Haram, ta hanyar wani shirin "Operation safe Corridor", inda za a sauya musu mugun tunanin da yake zukatansu da kuma ba su ayyukan yi.

Kuma a kwanan nan ne rundunar sojin ta ce ta sauya dabi'un 'Yan Boko Haram 95 da suka tuba bayan ta horar da su a karkashin shirin sauya tunaninsu.

Sannan tun a makon jiya ne rundunar sojin ta mika wasu 'yan boko Haram 244 ga gwamnatin Borno da za su shiga cikin al'umma bayan sauya tunaninsu da tabbatar da ingantuwar rayuwarsu.

Masana tsaro dai na ganin akwai sarkakiya a shirin inda suke bayyana fargaba kan ko mayakan da aka saka sun tuba ne har abada.

Wasu 'yan Najeriya da BBC ta zanta da su a garin Maiduguri da ke fama da rikicin Boko Haram, suna ganin shiri ne mai kyau yayin da kuma wasu ke ganin barazana ne ga al'umma.

A cewar wani mazauni Maiduguri, yana fatar wadanda aka yi wa laifi su yafe su kawar da kai daga 'yan Boko Haram da aka saka domin tabbatar da zaman lafiya.

"Abu ne wanda gwamnati ta yi don tausaya ma su da kuma zaman lafiya da ta ke kokarin tabbatar wa"

Wasu sun yi kira ga al'umma su kauracewa kyamatar mutanen, kada su kalle su a matsayin 'yan Boko Haram.

A cewar wani mazauni Maidguri, "Mutum kan iya zama dan iska a yau, gobe kuma ya zama malami".

Amma wasu 'yan Najeriyar sun ce ya kamata al'umma su yi taka-tsantsan musamman wajen yin hulda da mutanen da aka saki domin suna iya yin tubar mazuru don a sake su daga baya su cutar da jama'a.

"Yadda gwamnati ta sake su, to ta samar mu su da abin yi, ta hanyar ba su horo da jari", a cewar wani mazauni Maiduguri.

"Ba haka kawai a sake su ba daga baya kuma a manta da su, idan haka ta faru suna iya komawa yin abin da suke yi a da ko fiye ma da haka".

Labarai masu alaka