Dabbobi ma na da gidan marayu

Dabbobi ma na da gidan marayu

A kasar Kenya an ware wani gida da ake renon dabbobi marayu, wanda aka gina fiye da shekaru hamsin da suka wuce.

Masu yawon bude ido da dama kan yi tururuwa zuwa gidan domin debe kewa.

A wurare da dama a kan samu gandun namun dawa, amma ba kasafai ake samun gidan marayunsu ba.

A Kenya an dade da yi wa dabbobi wannan tanadin, tun a shekarar 1963.

Wakilin BBC Ibrahim Isa wanda ya ziyarci gidan marayun dabbobin a Kenya ya ce akwai asibiti da kwararrun likitoci a cikin gidan, har ma da motar daukar marar lafiyar saboda bukatar gaggawa.

Ya kuma ce, a gidan, an fi mayar da hankali ne wajen reno da goya dabbobin da aka kashe iyayensu, kuma wannan ne ma sa ake ganin jariran Zakoki da na Damisa da Birrai da Kuraye da sauran namun dawa.

Ya ce wani abun sha`awa shi ne yadda ake hada kananan zakoki da kuraye a keji daya, inda za a gan su suna wasa da juna.

Sannan ana jinyar dabbobin da aka raunata, da wadanda ke fama da rashin lafiya.

Galibi dai dabbobin da aka rena, sukan yi rayuwarsu ne daga kuruciya har su tsofe a gidan marayun, ba tare da sun koma daji ba.

Bayanan hoto,

Ana hada kananan zakoki da kuraye a keji daya

Lilian Ajouga jami`a a Gidan dabbobin daji marayu a Nairobi ta shaidawa wakilin BBC Ibrahim Isah cewa, "Akwai dabbobin da ake mayar da su daji".

"Amma dabbobi da ke rayuwa da nama irin su dangin Zaki da Damisa da Kura ba a mayar da su dawa saboda ba za su rayu a can ba, kasancewar ba su nakalci dabarar farauta daga iyayensu ba".

"saboda sun riga sun saba da zaman a tsakanin mutane, don haka mayar da su daji tamkar jefa su cikin hadari domin ba za su kai labari ba", a cewar jami'ar.

Gidan dabbobi marayun na cikin manyan kafofin samun kudin shiga a Kenya, kasancewar manya da yara daga bangarorin duniya kan ziyarci gidan.

Bayanan hoto,

Kenya na samun kudaden shiga ta hanyar masu zuwa yawon bude ido

Mataimakin shugaban kasar Burundi, Gaston Sindimwo wanda shi ma ya je cire kwarkwatar-idonsa a gidan marayun na dabbobi, ya shaidawa Ibrahim Isa cewa ya ji dadin zuwansa gidan domin babu irinsa a Burundi.

Daya daga cikin masu yawon bude ido da suka kai ziyara gidan marayun na dabbobi Justin Davies daga kasar Australia ya shaidawa BBC cewa yadda mutane ke kula da dabbobin da aka raunata da marasa lafiya da kuma marayu, abu ne da ya kayatar da shi.

"Abin kayatarwa ne yadda muka samu damar kusantar wadannan dabbobin, har ma muka taba jikinsu", a cewar Mista Davies.

Kasar Kenya na samun kusan kashi 15 bisa dari na girman tattalin arzikinta ne daga yawon bude ido samakon musamman a irin wannan bangare na samar gandun daji.

Kuma akalla mutum guda daga cikin mutum goma a kasar na samun aikin yi a wannan harka.

Masana sun bayyana cewa akwai wuraren da za su dace da harkar yawon bude ido a kasashen Afirka da dama, wadanda ba lallai sai namun daji ba, wadanda idan gwamnatocinsu suka yi koyi da Kenya, za su ci irin wannan gajiyar.