Sakin Zakzaky ba zai hana gwamnati daukaka kara ba- Kotu

Zakzaky
Image caption An fara sauraren karar da gwamnatin Tarayya ta daukaka kan sakin Zakzaky

Kotun daukaka kara a Najeriya ta fara sauraron karar da gwamnatin tarayya ta daukaka, a kan hukuncin da wata babbar kotun kasar ta bayar da umurnin a saki shugaban kungiyar 'yan uwa musulmi ta 'yan shi'a na kasar.

Gwamnatin na ci gaba da tsare El Zakzaky ne, duk da umarnin babbar kotun kasar da ta ce a sake shi a watan disamban shekarar 2016.

Alakalan kotun uku ne suka saurari karar a ranar Litinin wadda gwamnatin Najeriya da wasu hukumin tsaro da suka hada da hukumar tsaro ta farin kaya ta DSS da rundunar 'yan sandan kasar da kuma ministan shari'a Abubakar Malami suka daukaka.

A yayin zaman kotun, Lauyan gwamnatin Najeriya, Oyi Kolishon ya bukaci kotun ta ba su damar gyara wasu takardu da suka shafi karar da suka daukaka.

Sai dai lauya mai kare jagoran 'yan shi'a Femi Falana ya mayar da martanin cewa, kotun ba za ta saurari gwamnatin Tarayya ba idan ba a saki wanda yake karewa ba.

Falana ya ce ba zai yiwu gwamnati ta zo da wata bukata a wata kotu ba, bayan kin mutunta umurnin babbar kotu.

Mai shari'a Mojeed Owoade wanda ya jagoranci zaman kotun da kuma mai shari'a Chidiebere Uwa sun nuna rashin jin dadinsu kan yadda gwamnati ta ki mutunta hukuncin kotun kasar, abin da suka ce bai da ce ba.

Alkalan kotun sun bayyana cewa sakin El Zakzaki ba zai hana gwamnati ta daukaka karar ba.

Lauyan da ke kare gwamnati, Mista Koloshon ya bukaci kotun ta ba su damar mayar da martani.

Amma Femi Launa ya shaida wa kotun cewa," Ministan shari'a na kasar, Abubakar Malami ya fito fili ya bayyana cewa gwamnatin ba za ta bi umarnin daukaka karar ba.

A shari'ar da aka fara saurare dai, Jagoran kungiyar 'yan Shi'ar Ibrahim El Zakzaki bai samu halartar zaman kotun ba.

Sannan kotun ba ta tsayar da wata takamammiyar ranar da zata ci gaba da sauraren karar ba.

Gwamnatin dai na tsare da Malam Ibrahim El Zakzaky tun a shekarar 2015 bayan an samu wani tashin hankali tsakanin magoya bayansa da sojojin kasar a garin Zaria, lamarin da ya kai ga mutuwar daruruwan 'yan shi'a.

Labarai masu alaka