'Kannen miji sun kashe matar yayansu a Katsina'

Katsina Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Rundunar 'Yan sandan jihar Katsina ta kama kannen mijin guda biyu

Wata takaddamar zamantakewa tsakanin uwar miji da sarukarta wato matar danta, ta kai ga kannen miji sun yi sanadin ajalin matar yayan nasu.

Wannan al'amari ya faru ne ranar Lahadi a karamar hukumar Dan Ja a jihar Katsina da ke arewacin Najeriya.

Matar mai suna Hadiza Salisu Dan kasuwa, ta samu matsala ne da surukarta da suke zama tare a gida guda da mijinta a garin Layin Mahuta da ke cikin karamar hukumar Dan Ja.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Katsina Gambo Isa, wanda ya tabbatar wa da BBC faruwar lamarin, inda ya ce bayanan da suka tattara sun nuna cewa cacar-baki aka yi tsakanin matar da uwar mijinta.

Ya ce, uwar mijin ce ta yi zargin cewa surukar tata ta zage ta, dalilin da ya sa kannen mijin biyu, Shafi'u Ibrahim da Fahad, suka fusata a kan an zagi mahaifiyarsu.

A cikin dare suka je suka sami matar yayan nasu suka ma ta duka da itace har sai da ta kai tana zubar da jini har ta rasu" kamar yadda 'yan sandan suka tabbatar.

An dauki gawarta an kai babban asibiti na Funtua, inda likitoci suka tabbatar da mutuwarta.

An yi jana'izar matar a ranar Litinin 22 ga watan Janairu.

Hadiza Salisu Dan kasuwa, sun haifi 'ya'ya hudu da mijinta da ke aiki a Abuja.

Mahaifinta Malam Salisu Dan Kasuwa, ya shaida wa BBC cewa an dade tana samun matsala da uwar mijinta, har sai da ta kai tana yin yaji domin a raba su da ita.

Ya ce, yadda mijin ya nuna yana matukar sonta, shi ne dalilin da ya sa suke fada da uwar mijin, har ta ke kishi da ita.

Sannan idan mijin zai ba ta abu, uwar ce ke karba ta ba ta.

"Wannan mummunan al'amari ya faru ne kwana daya da komawarta gidan miji bayan mai unguwa ya shiga tsakani an sasanta" a cewar mahaifin Hadiza.

Ya kuma ce, bayan ta koma ne daga baya rikici ya kaure tsakaninta da uwar mijin.

Kuma a cewarsa, ba su samu labarin mutuwar Hadiza ba daga dangin mijin sai ranar Litinin washe-garin faruwar lamarin bayan 'yan sanda sun kama kannen mijin da suka yi sanadin mutuwar 'yarsa.

Yanzu dai 'yan sanda na ci gaba da gudanar da bincike bayan sun kama kannen mijin biyu wadanda yanzu ake tsare da su a hedikwatar 'yan sanda da ke Katsina.

Labarai masu alaka