Me ya sa ma'aikata ke kokawa da watan Janairu?

Ma'aikata a Najeriya, na shiga halin oh ni 'ya su a watan Janairu Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ma'aikata a Najeriya, kan shiga halin oh ni 'ya su a watan Janairu

Watan Janairu na dukkan shekara akasari kan kasance mai wahalar gaske ga ma'aikata a Najeriya.

Biyan albashi da wuri a watan Disamba, kan mayar da watan Janairu mai tsawo da wahala ga ma'aikaci fiye da kowanne wata a shekara, a yayin da suma 'yan kasuwa kan fuskanci koma baya a ciniki.

Mal. Hassan L. Adamu, ma'aikaci ne a daya daga cikin ma'aikatun gwamnatin jihar Kaduna, ya shaida wa BBC cewa, biyan albashin da ake yi da wuri a watan Disambar kowacce shekara saboda bukukuwan kirsimeti da sabuwar shekara, shi ya sa ake shiga halin ka-ka-ni-kayi a kowacce farkon shekara.

Malam L Adamu, ya ce ma'aikata kan shafe kwana 40 ba bu albashi tun daga lokacin da aka biya na Disamba zuwa karshen watan Janairu.

Ya ce wannan dogon lokaci da ake dauka kafin biyan albashi, na jefa da yawan ma'aikatan Najeriya cikin wahala, domin a cewarsa yawanci a duk sabuwar shekara ana biyan kudin makarantar yara da kudin hayar gida da dai makantansu.

Malam L. Adamu, ya ce a irin wannan yanayi ma'aikata ba su da wata mafita illa su ci bashi, wani lokacin ma idan mutum ya je neman bashi ba lallai ya samu ba.

Ma'aikatan Nigeria sun kusa samun karin albashi

Buhari ya caccaki gwamnoni kan albashi

Ma'aikatan sun ce ko a wajen aiki abincin da za su saya su ci ma, bashi suke karba kafin a biya albashi, domin su kansu masu sayar da abincin idan ba su bayar bashin ba, to sai dai su koma da abinsu gida.

'Yan kasuwa ma ana su bangaren, sun ce suna samun karancin ciniki a kowanne watan Janairu na farko shekara, saboda a cewar wasu 'yan kasuwa da BBC, ta zanta da su sun ce dama ma'aikata sune karfin ciniki, to tunda ba albashi dole suma suna ji a jikinsu.

Ma'aikata dai kan kira watan Janairu da suna wata na 40, saboda yadda ake shafe kwana 40 ba bu albashi.

Labarai masu alaka