Kun san iyalan da suka shafe wata uku suna kwana a filin jirgi?

Thai airport officials talk to members of a Zimbabwean family Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Iyalan sun ce suna fuskantar cin zarafi ne a Zimbabwe don haka ba za su koma can ba

Idan kun taba yin korafin yadda aka tursasa muku kwana a filin jirgin sama bayan an bata muku lokaci, to watakila za su sake tunani idan ku ka ji labarin wasu iyalai 'yan Zimbabwe, wadanda suka samu komawa kasarsu bayan da suka shafe wata uku suna kwana a filin jirgin saman Suvarnabhumi na kasar Thailand.

Iyalan, wadanda hudu daga cikin su manya ne, hudu kuma yara 'yan kasa da shekara 11 sun isa birnin Bangkok ne na kasar Thailand tun a watan Mayun 2017.

Sun yi kokarin barin kasar a watan oktoba don wucewa Sipaniya, amma sai suka gano cewa ba su da takardun izinin shiga Sipaniyar.

An hana su sake shiga kasar Thailand din saboda sun kammala adadin kwanakin da aka ba su izinin yi, kuma hakan zai sa sai sun biya tara.

Amma kuma sai suka ce su ba za su koma Zimbabwe ba saboda suna fuskantar cin zarafi.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Iyalan sun yi ta rayuwa a filin jirginThe family had been living in Suvarnabhumi airport since May

An gano halin da iyalan ke ciki ne bayan da wani ma'aikacin filin jirgin Suvarnabhumi ya wallafa hotonsa da na daya daga cikin yaran iyalan a watan Disamba, yana cewa; "suna rayuwa a nan saboda wasu matsaloli da suke fuskanta a kasarsu."

A wancan lokacin jami'ai sun bayyana cewa za su taimaka wa iyalan ta hanyar shirya musu tafiya Dubai ta bin kasar Ukraine da taimakon hukumar zirga-zirgar jiragen sama ta Ukraine UIA, daga can kuma sai su samu wucewa Turai.

Amma mai magana da yawun hukumar UIA din ya ce iyalan sun soke tikitin yin wannan tafiya, abun da ya sa aka sake dawo da su Thailand daga Dubai.

Iyalan sun roki taimako daga Majalisar Dinkin Duniya, suna tsoron cin zarafi ne a Zimbabwe, bayan abun da ya faru a watan Nuwamba na tsige Shugaba Robert Mugabe.

MDD ta ce a wancan lokaci tana neman zabi. Thailand dai ba ta bai wa masu neman mafaka iznin zama a kasar.

Hakan ce ta sa iyalan suka yi ta zama a bangaren masu tafiya na filin jirgin, inda ma'aikatan wajen suka dinga kula da su.

Wani mai magana da yawun hukumar shige da fice ta kasar ya ce a ranar Litinin 22 ga watan Janairu ne iyalan suka bar kasar a karshe.

Wani babban jami'in 'yan sanda ya shaida wa BBC cewa iyalan sun bar Thailand zuwa Philippines.

Akwai wani sansanin 'yan gudun hijira a can, amma babu tabbas ko za su zauna a can ne ko kuma za a sake kai su wani wajen.

Sai dai mai magana da yawun Hukumar 'yan gudun hijira ta MDD ta ce ba za ta ce komai a kan wannan batu ba.

Labarai masu alaka

Karin bayani