'Yan sandan Abuja sun musanta kama 'yan BBOG

BBOg Hakkin mallakar hoto BBOG Twitter
Image caption A yanzu haka dai da dama daga cikin mambobin BBOG kamar su tsohuwar ministar ilimi Oby Ozekwesili da Aisha Yesufu suna rundunar 'yan sandan birnin tarayya a tsare

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta musunta kama wasu jagororin kungiyar da ke fafutukar ganin an sako 'yan matan Chibok ta BringBackOurGirls, kamar yadda aka ruwaito tun da farko.

A wata sanarwa da ta fitar, rundunar 'yan sandan babbar birnin Tarayya Abuja ta ce an kawo su ne kawai domin tabbatar da bin doka da oda, bayan da wasunsu suka tarwatsa shingen binciken jami'an tsaro da aka kafa domin hana su yin zanga-zanga a dandalin Unity Faountain.

Sanarwar ta ce bayan sun gana da kwamishinan 'yan sandan Abuja Sadiq Abubakar Bello, 'yan kungiyar ta BringBackOurGirls, nan take ne kuma suka fice daga ofishin na 'yan sanda.

Dandalin Unity Fountain, ya kasance inda 'yan kungiyar ke yawan zama don tunawa hukumomi batun ceto 'yan matan Chibok.

Aisha Yesufu daya ce daga cikin manyan jagororin kungiyar, ta kuma shaida wa BBC cewa sun taru a dandalin ne da zummar yin tattaki zuwa fadar shugaban kasa domin tuna masa cewa har yanzu akwai sauran 'yan matan Chibok 112 da ke hannun kungiyar Boko Haram, "kuma ya zama wajibi gwamnati ta kara kaimi don ceto su," in ji ta.

"Amma sai 'yan sanda suka hana mu fita daga dandalin suka hana mu yin tattakin duk kuwa da cewa mun cika sharuddan da doka ta tanada kafin yin duk wani maci, amma ga mamakinmu sai aka hana mu wannan damar.

"To hakan ce ta sa 'yan sandan suka kama mambobinmu da dama har da wadanda suka yi niyyar gudu don tsira."

Hakkin mallakar hoto BBOG Tiwtter

Labarai masu alaka