Me 'yan Nigeria ke cewa kan wasikar Obasanjo ga Buhari?

Muhawara ta barke tsakanin 'yan Najeeriya kan wasikar da Obasanjo ya rubutawa Buhari Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Muhawara ta barke tsakanin 'yan Najeeriya kan wasikar da Obasanjo ya rubutawa Buhari

Wasikar da tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo ya fitar a ranar Litinin inda yake bai wa Shugaba Buhari shawara cewa kar ya sake yin tazarce a 2019 ta jawo muhawara mai zafi a tsakanin 'yan kasar.

Muhawarar ta barke a shafukan sada zaumunta da ma kafafen watsa labarai daban-daban inda mutane ke ci gaba da tofa albarkacin bakinsu.

A cikin bwasikar wacce Obasanjo ya aikewa manema labarai, ya caccaki Shugaba Buhari da cewa kamata ya yi ya bar mulki a 2019 ya je ya huta saboda yawan shekaru da yanayin lafiyarsa.

Ya kuma fiddo da wasu abubuwa da ya kira nakasu da kasar ke fuskanta wadanda a dalilinsu ne a zaben 2015 mutane suka fita kwai da kwarkwata don zabar Buhari da yakinin cewa shi ne zai magance musu wadannan matsaloli, "amma sai ga shi ba ta sauya zani ba," in ji tsohon shugaban kasar.

A baya dai Obasanjo ya sha yabawa Buhari kan sha'anin mulkinsa.

Buhari ya yi tsufa da sake tsayawa takara - Obasanjo

Buhari ya jefa Nigeria a halin koma-baya —Fasto Bakare

A shafukan Twitter da Facebook dai mutane sun ta bayyana ra'ayoyinsu inda wasu ke ganin lallai maganganun Obasanjo gaskiya ne kuma a kan hanya suke.

JJ Omojuwa wani fitaccen mai amfani da shafin twitter ne ya kuma rubuta cewa: "Argh! Lallai wannan alama ce da ke nuna cewa 2019 ta sako kai. Obasanjo bai taba fadar magana irin wannan a kan shugaban kasa kafin zabe ba kuma ba ta faru ba. Ga 'yan kallo irin ku da dama, za ku iya cewa lallai wannan ce shimfida ta abun da zai faru a zaben 2019."

Hakkin mallakar hoto Omojuwa Twitter

Wasu kuwa cewa suke lallai Mista Obasanjo bai taba faduwa wani zabe da shi ya tsaya takara ko ya marawa wani baya ba tun daga shekarar 1999 da 2003 da 2007 da 2011 da kuma 2015.

Da zabukan da ya tsaya karkashin PDP guda hudu, da wanda ya marawa APC baya guda daya, a yanzu kuma ga shi ya nuna alkiblarsa ba tare da marawa ko wacce jam'iyya baya ba. Ko me zai faru?

Ita ma Nedu Okeke wacce take shafin Twitter da sunan @Nedunaija got=yon bayan wasikar ta yi da cewa: "Obasanjon da ya mara maka baya a 2015 ma ya ba ka shawara da cewa kar ka sake tsayawa takara saboda gazawarka.

"Matarka da ta goyi bayanka a 2015 ma ta nuna alamar cewa ba za ta sake goyon bayanka ba. Baba, don Allah ka tafi gida."

Hakkin mallakar hoto Twitter

Masu sukar wasikar Obasanjo

Kazalika a hannun guda kuma akwai dumbin mutanen da suke sukar Obasanjo kan wannan wasika da ya aike wa Buhari.

@abubakar471 ya rubuta cewa: "Idan har obasano zai tsayar mana da 'yan takara sau uku, kuma dukkansu ba shugabanni na-gari ba ne, to don me ya sa zan gaskata son ransa a yanzu?"

Wani kuwa mai suna Parodidant Buhari a Twitter ya rubuta cewa: "Ga dukkan alamu Obasanjo bai san cewa bai yi tsufa da shiga gidan yari ba."

Me jam'iyyun siyasa ke cewa?

Babbar jam'iyyar adawa ta PDP a nata martanin cewa ta yi: Tsohon shugaban Najeriya ya tabbatar da matsayin da muka dade a kansa cewa gwamnatin Buhari da APC sun gaza a ko wanne fanni.

"Sai dai muna kira ga mutane da kar su yarda da kirkiro wata sabuwar kungiyar siyasa kamar yadda ake ta kira, maimakon haka gara su marawa PDP baya don ta ceto su."

Shi kuwa shugaban jam'iyyar APGA Dr. Victor Oye, cewa ya yi "Dr. Obasanjo bai cancanci shawartar Buhari kar ya sake tsayawa takara ba, kuma ya daina jawo tayar da hakarkari ba gaira ba dalili."

Wannan dai ba shi ne karo na farko da Obasanjo ya taba aikewa wani shugaban kasa wasika cewa kar ya yi tazarce ba, a baya ma ya taba aikewa tsohon Shugaba Goodluck Jonathan wasika cewa kar ya yi ta-zarce a 2015.

Wannan batu dai zai ci gaba da jan hankalin 'yan Najeriya a ciki da wajen kasar, sai dai babu tabbas ko wannan kira na Obasanjo zai yi tasiri ko ba zai yi ba, musamman ganin cewa wannan shekara ta 2018 ita ce wacce za a bambance tsakanin aya da tsakuwa kafin zaben 2019.