Wadanne 'kura-kurai' Buhari ya tafka tun hawansa mulki?

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Kalli ra'ayoyin 'yan Najeriya game da wasikar Obasanjo ga Buhari

Tsohon Shugaban Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya ce 'yan Najeriya sun yi tururuwar zaben Shugaba Buhari ne a 2015 saboda gazawar tsohon Shugaba Goodluck Jonathan ta bangarori da dama.

Sai dai ya ce har yanzu ana fama da matsalolin da aka yi fama da su lokacin mulkin Mista Jonathan din ba tare da samun sauyi ba.

Matsalolin kuwa da ya lissafa sun hada da rashin taka rawar gani a wajen gudanar da al'amuran gwamnati, da talauci, da rashin tsaro, da gazawa wajen kyautata tattalin arziki, da bai wa wasu na kusa da shi mukamai da sakaci wajen tafiyar da aiki.

Ya kara da cewa akwai kawar da kai yayin da ake aikata ba daidai ba da rashin hadin kan kasa da rashin tafiyar da siyasar cikin gida yadda ya dace da kuma karuwar bambance-bambance tsakanin masu hali da marasa galihu.

Sai dai Cif Obasanjo ya ce baya ga wadancan matsaloli, akwai wasu bangarori guda uku da gazawar Buhari ta fito fili ba kamar yadda aka zata ba.

"Ta farko ita ce bai wa na kusa da shi mukamai da ya yi daidai da mutum ya debo 'yan kabilarsa ya damka musu komai. Wannan ya yi mummunan tasiri a kan tafiyar da sha'anin mulkinsa wanda haka bai haifar wa kasar alheri ba.

"Ya ya za a bayyana badakalar mayar da Abdulrashid Maina bakin aiki? Batutuwa irin wannan nawa aka boye aka ki bayyana wa al'umma?" a cewar Obasanjo.

Wasikar ta ci gaba da cewa gazawa ta biyu daga Buhari ita ce rashin iya tafiyar da siyasar cikin gida yadda ya dace.

"Wannan al'amari ne da ya sa aka kara samun rarrabuwar kawuna a kasar da kuma karuwar bambance-bambance tsakanin masu hali da marasa galihu. Hakan ya yi matukar tasiri ga tsaron kasar."

"Gazawa ta uku ita ce yadda yake dora laifukan gazawarsa a kan wadansu. Alal misali, yadda yake zargin gwamnan babban bankin Najeriya da rage darajar naira da kashi 70 cikin 100, da kuma zargin gwamnatocin baya da hakan.

"Kar mu bari wani ya yaudare mu, tattalin arziki ya ta'allaka ne akan siyasa, saboda haka tun da siyasarmu ta shiga halin ni-'yasu, dole tattalin arzikinmu ya shiga halin ha'ula'i.

"Idan da a ce komai yana tafiya yadda ya kamata to da ba za mu bukaci Shugaba Buhari ya shigo cikin tafiyar ba ma."

Ba Cif Obasanjo ne kawai mutumin da ya taba fitowa karara ya bayyana gazawar Shugaba Buhari ba, ko a baya ma an taba samun mutanen da a baya na kusa da shi ne da suka soke shi kan mulkinsa.

Hakkin mallakar hoto TWITTER/TUNDE BAKARE

A baya-bayan nan ma mutumin da ya tsaya takarar mataimakin shugaban kasa tare da Muhammadu Buhari a shekarar 2011, Fasto Tunde Bakare, ya ce gwamnatin Buharin ta jefa Najeriya a halin ci baya maimakon ci gaba.

A cewarsa, "Wannan gwamnatin ta kafu ne a jigo uku, wadanda suka hada da magance matsalar tsaro da samar da ayyuka da yaki da cin hanci, amma idan ka duba babu abin da za ka gani sai alamomin ci gaba.

Haka shi ma Buba Galadima wanda yana daya daga cikin jigogin da aka kafa jam'iyyar APC da su, tare da kasancewa na gaba-gaba wajen fafutukar ganin Shugaba Buhari ya samu mulkin Najeriya, ya ce bai gamsu da kamun ludayin gwamnatin ba.

A kwanakin baya ya shaida wa BBC cewa a yanayin salon jagorancin jam'iyyar da kuma mulkin da ake yi a kasar a yanzu, lamarin ya ba su mamaki domin sun yi zaton za a samu gagarumin sauyi a kasar zuwa yanzu, amma hakan ba ta kasance ba.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Buba Galadima ya ce Buhari ya yi watsi da jama'arsa na asali

Baya ga mutanen da a da suke marawa Shugaba Buhari baya ma, akwai mutanen da har a yanzu suke da kusanci da shi amma kuma suka fito fili suka fadi wasu kura-kurai da a cewar su in har bai gyara su ba to fa ba lallai ya samu nasarar zarcewa a mulkin ba a 2019.

Daya daga cikin wadannan mutane su ne matarsa Aisha Buhari, wadda a karshen shekarar 2016 a wata hira da BBC Hausa ta ce, wasu 'yan tsirarun mutane sun mamaye gwamnatin mijinta, inda suke hana ruwa gudu.

Duk da cewa Aisha ba ta bayyana sunayen mutanen ba, sai dai ta ce 'yan Nigeria sun sansu kuma "tana tsoron boren da za su iya yi."

Uwargidan shugaban kasar ta kara da cewa shugaba Buharin ya yi watsi da wadansu 'ya'yan jam'iyyar APC wadanda suka sha wahala da mijin nata a lokacin gangamin yakin zabe.

Me masu sharhi ke cewa?

Mai sharhi kan harkokin siyasa a Najeriya Dokta Abubakar Kari, ya ce daya daga cikin kuskuren shugaban shi ne, "rashin nakaltar dimokradiyyar cikin gida saboda nada wadansu mutane na kut da kut, misali gaba daya manyan jami'an tsaro 'yan Arewa ne kuma Musulmi ne."

Hakazalika ya ce, "akwai mukamai da dama da aka bai wa wadansu da ake ganin suna da dangantaka ta jini ko auratayya da shugaban, kamar Ministan albarkatun Ruwa na kasar Husseni Adamu."

Masanin ya ce yawancin masu fada a ji na fadar shugaban kasa suna da alaka da shi,"amma a gwamnatocin baya ba haka abin yake ba don za ka ga mutane ne daga sassan Najeriya daban-daban."

Dangane da batun dorawa gwamnatocin baya laifi, Dokta Kari ya ce masu magana da yawunsa suna yawan dora laifi ga gwamnatocin da suka gabata.

Ya ce mutane suna kafa hujja da cewa saboda haka ne aka zabe shi wato saboda ana tunanin Buhari zai iya kawo gyara, masanin ya ce wannan ya sa jama'a kin gamsuwa da uzurin gwamnatinsa.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption 'Yan Najeriya sun yi tururuwar zaben Shugaba Buhari a 2015 don ya share musu hawaye kan matsalolin da suka samu kansu a ciki

Dokta Kari ya kara da cewa shugaban ya nesanta kansa daga talakawa, "amma a lokacin neman zabe talakawa na da yakinin cewa shi nasu ne don zai share musu hawaye amma sai aka samu akasin hakan."

Har ila yau masanin ya ce "cin hanci ya ragu a kasar amma kuma ba a daina ba."

Ya kuma ce "ba a daina daukar ma'aikata ta bayan gida ba. Na kusa da shi na cin karensu ba babbaka kuma ba abin da ake yi, ko abin ya fito fili ba ya daukar wani mataki."

"Hakan ce tasa wasu ke ganin Buharin ne kuwa?" In ji shi.

Tasirin hakan a zaben 2019

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Kalli Muhawarar masana kan wasikar Obasanjo

Dokta Kari ya ce "gaskiya ni ina ga idan abubuwa suka ci gaba yadda suke a yanzu, to za su yi tasiri kan sake tsayarwarsa takara a zaben shekarar 2019."

Daga nan ya ce, "a baya irin wannan abuwane ne suka jawo aka ki sake zabar gwamnatin PDP."

"Magoya bayan Buhari da dama a ciki da wajen kasar jikinsu ya yi sanyi. Idan ba a yi hankali ba da dama ba za su fito zabe ba, wadansu kuma za su iya zabar abokan adawarsa."

Ko lokaci ya kure wa Buhari?

Sai dai masanin ya ce lokaci bai kure wa shugaban ba, "don zai iya yin gyara."

"Zai iya gyarawa tun da akwai sauran kusan watanni 15, muddin ya yarda an yi kuskure, kuma aka dauki matakin gyara to zai iya yin nasara.

"Amma idan dai aka ci gaba a yadda ake yanzu to zai iya shan kaye a 2019," in ji shi.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wasu masana na cewa APC ta samu galaba kan yaki da Boko Haram wanda yana cikin alkawuran yakin neman zabe da ta yi

Labarai masu alaka