Harin sama na Amurka ya hallaka 'yan IS 150

File photo showing US-led coalition air strike on IS position in the Syrian city of Raqqa on 15 August 2017 Hakkin mallakar hoto Reuters

Rundunar sojin hadaka da Amurka ke jagoranta wadda ke yaki da kungiyar IS ta ce ta kashe mayakan kungiyar 150 a wata hedikwatar kungiyar da ke Siriya.

Wata sanarwa ta ce an kaddamar da harin ne ranar Asabar kusa da al-Shafa a kogin da ke tsakiyar tsaunin Euphrates a kudu maso gabashin lardin Deir al-Zour.

Sanarwar ta kara da cewa bayanan sirri da aka tattara da kuma sa ido da ake a wajen sun nuna cewa babu wani farar hula da abun ya shafa.

Babu wani tabbaci kan harin daga bakin kungiyar IS ko magoya bayanta.

Rundunar sojin hadaka da Amurka ke jagoranta ta ce kungiyar IS ta yi asarar kashi 98 cikin 100 na yankinta da ta kwace daga Iraki da Syria a 2014, a lokacin da ta yi ikirarin kafa daular musulunci.

A yanzu yankin da IS ke iko da shi ba shi da wani girma a Siriya, inda ya hada da wani bangare na tsaunin Euphrates, wanda rundunar sojin hadaka da Amurka ke jagoranta ta kai wa hari.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Yadda IS ke ci gaba da zama annoba a Iraki

Sanarwar rundunar sojin hadakar ta ce hare-haren saman da aka kai hedikwatar IS din ya zo ne bayan samun wasu bayanan sirri kan wajen.

Ta kuma kara da cewa mayakan IS din sun yi ta tururuwar guduwa daga hedikwatar tasu bayan da aka kai harin, wanda ya yi sanadin mutuwar tsakanin mutum 145 zuwa 150.

Labarai masu alaka