An kai wa kungiyar agaji ta Save the Children hari

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Harin ya sa bakin hayaki ya turnuke yankin baki daya

Maharan sun tayar da abubuwa masu fahsewar ne kafin daga bisani su shiga ofisoshin ma'aikatan agaji na kungiyar Save the Children a birnin Jalalabad na gabashin Afghanistan.

A kalla mutum biyu ne suka mutu, wasu 12 kuma suka jikkata in ji jami'ai. An yi amannar cewa kusan mutum 50 ne suke cikin ginin ofishin a lokacin faruwar abun.

Kungiyar IS ta ce uku daga cikin mayakanta ne suka kai harin.

A yanzu haka dai kungiyar Save the Children ta dakatar da ayyukanta a Afghanistan na wucin-gadi.

Ya ya harin ya faru?

Harin ya faru ne da karfe 9 na safiyar kasar a ranar Laraba, a yayin da wani dan kunar bakin wake ya tayar da bam a wata mota a gaban mashigar ofishin Save the Children, kamar yadda wani mai magana da yawun gwamnan lardin Nangarhar Attaullah Khogyani, ya shaida wa BBC.

Wani ganau da ke cikin ginin lokacin da abun ya faru ya shaida wa kamfanin dillancin labarau na AFP cewa ya ga wani dan bindiga yana dukan kyauren shiga ginin da wata roka.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani dan kunar bakin wake ya tayar da bam a wata mota a gaban mashigar ofishin Save the Children,
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Jami'an tsaro sun sun yi wa yankin kawanya

Kwamandojin sojin Afghanistan sun hada kai da 'yan sanda don kokarin kawo karshen harin.

Kusan mutum 45 aka ceto daga ginin da ke kasan ofishin, yayin da aka ci gaba da gwabza fada a saman bene.

Tun da fari dai AFP ta ruwaito cewa wani ma'aikaci ya aiko da sakon Whatsapp da ke cewa" Ina jin maganganun wasu mahara biyu.... Suna neman mu. Ku yi mana addu'a... Ku gayawa jami'an tsaro.'

Akwai wasu kungiyoyin agajin da dama a wannan yankin, da kuma ofisoshin gwamnati.

Labarai masu alaka