Maganin karfin maza ya kusa kai wasu lahira

Annobar ta tayar da hankali mutane sosai a kasar Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Annobar ta tayar da hankali mutane sosai a kasar

An kwantar da wasu maza uku a asibiti sakamakon barkewa da amai da guduwa mai tsanani, bayan da suka sha magungunan kara karfin maza a Zambiya.

Daga farko dai an yi tsammanin sun kamu da kwalara ne sai daga baya aka gano cewa magungunan kara karfin mazan ne suka yi musu illa.

Tun a shekarar da ta gabata ne kasar Zambiya ke fama da matsananciyar annobar kwalara da ta yi sanadin kashe mutum 70, inda aka samu wadanda suka kamu da ita fiye da 3,000.

Amma akwai alamun cewa mutum ukun wadanda 'yan yankin gabashin kasar ne, ba sa daga cikin masu fama da annobar.

A maimakon haka, sai aka gano cewa sun yi ta dirkar maganin karfin maza ne wanda ake kira da mvubwe.

Babban jami'in gwamnati na yankin Chanda Kasolo, ya shaidawa BBC cewa, nan da nan mutanen suka fara amai inda aka garzaya da su cibiyar masu kula da kwalara.

Bayan da aka yi musu gwaje-gwaje sai aka gano cewa maganin karfin maza da barasa da kuma abincin da suka ci ne suka hadu suka zame musu guba a ciki, har aka yi tsammanin kwalara ce.

Amma bayan da aka kara yin wasu gwaje-gwajen da yi musu tambayoyi, sai aka gano cewa magungunan karfin mazan ne suka fi yi musu illa.

Ya ce marasa lafiyar har yanzu suna cibiyar da ake kula da masu kwalarar, kuma sun fara farfadowa.

Labarai masu alaka