An kama 'faston' da ya halasta zina da shan giya a Tanzania

Fasto

'Yan sanda a Tanzaniya sun kama wani da ya kira kansa fasto bayan an gan shi a wani bidiyo inda yake rawa da kwalaben giya da kuma ikirarin cewa littafin baibil ya halatta shan giya da zina.

Gwajin lafiyar da aka yi wa mutumin mai suna Onesmo Machibya, mai shekara 44, wanda aka fi sani da suna Manzo Tito, ya nuna cewar yana da tabin hankali, in ji Gilles Muroto, kwamandan 'yan sanda a babban birnin kasar, Dodoma.

Kawo yanzu dai Mista Machibya ko kuma wakilansa ba su yi magana ba.

Bidiyon da aka yi ta yayatawa a shafukan sada zumunta sun nuna mutumin da ke ikirarin cewa shi manzo ne yana rawa kuma yana sumbatar matarsa da wata matashiya, yana mai cewa babu matsala mutum ya yi jima'i da matar da ba tasa ba.

'Yan sanda sun zarge shi da bayar da takardu a wuraren shakatawa da kuma wuraren sayar da barasa a Dodoma, da kuma yayata akidar da ta yi hannun riga da al'ada da dabi'un Tanzaniya.

Labarai masu alaka