An saki bidiyon yadda aka kashe sojojin Amurka a Niger

American soldiers Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An yi jana'izar sojojin da suka mutu a Amurka

Rundunar sojin Amurka ta ce tana kokarin tantance bidiyon da ake yayatawa a kafafan Intanet wanda ke ikirarin nuna gawarwakin sojojin Amurka bayan an kai musu hari a Nijar a shekarar da ta gabata, in ji kafar watsa labarai ta The Hill.

Wata sanarwar da rundunar sojin Amurka a Afirka (USAFRICOM) ta fitar ta ce: "Muna nazari a kan bidiyon kuma muna kokarin tantance gaskiyar sakon na Twitter da kuma ikirarin cewa bidiyo ne na kisa."

Sanarwar ta kara da cewa, rundunar ba za ta kara cewa komai ba game da lamarin har sai an kammala bincike.

Ranar 4 ga watan Oktobar bara ne dai aka yi wa sojojin Amurka 12 da kuma sojojin Nijar 30 kwanton bauna a kauyen Tongo da ke kudu maso yammacin kasar, wurin da ke da tazarar kilomita 240 daga babban birnin kasar, Niamey.

Rahotanni sun ce kimanin masu kaifin kishin Islama 50 dauke da manyan bindigogi ne suka yi wa sojojin kwanton bauna.

Wani mai bincike ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, wata kungiya mai alaka da kungiyar IS ta fitar da wani bidiyo, kuma ya kara da cewa bidiyon ya nuna sojojin da suka ji ciwo da kuma gawarwakin sojojin Amurka.

Rahotanni dai sun ce sojojin sun je neman bayanai ne game da wani babban mai tayar da kayar baya a yankin.

Amurka tana da kimanin sojoji 800 a yankin, in ji kafar The Hill .

Labarai masu alaka