Me ya sa 'yan BH suka fi kai hari a watan Janairu?

Boko Haram militants launched their insurgency in 2009 Hakkin mallakar hoto Boko Haram
Image caption Kungiyar Boko Haram ta fara hare-hare a shekarar 2009

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nanata cewa gwamnatinsa ta sami galaba kan kungiyar Boko Haram, amma binciken da BBC ta yi ya bayyana cewa lamarin bai sauya ba.

Binciken da BBC ta gudanar ya bayyana cewa kungiyarta hallaka fiye da mutum 900 a 2017, wanda kadan ya wuce yawan wadanda ta kashe a 2016.

Kungiyar ta kai hare-hare a duk tsawon shekarar, wanda ya ci karo da ikirarin shugaba Buhari da yake cewa an sami galaba akan maharan.

Mun duba alkaluman cikin natsuwa, kuma mun fitar da wani jerin bayanai, da irin hare-haren na Boko Haram daki-daki, da kuma wuraren da suka fi kai wa hari, kana mun duba wane wata ne suka fi kai hare-hare a ciki.

Su wane ne Boko Haram?

Boko Haram ta fara tayar da kayar baya ne a 2009 bayan da ta fara kai hare-hare a wani yunkurin kafa wata daula ta musulunci a yankin Afirka ta yamma.

Rikicin da ya biyo baya ya fi kamari a yankin arewa maso gabashin kasar kuma ya janyo mutuwar mutum akalla 20,000 kuma ya tarwatsa wasu mutum miliyan biyu daga muhallansu.

Hakkin mallakar hoto AFP/GETTY IMAGES
Image caption Birnin Maiduguri ya kasance wata cibiya ta rikicin na Boko Haram

A karkashin jagorancin Abubakar Shekau, Boko Hrama ta yi wa kungiyar IS mubaya'a a watan Maris na 2015.

A watan Agustan 2016 kungiyar ta dare, inda aka sami bangarori daban-dabam, bayan da kungiyar ta IS ta bayyana cewa an tunbuke Shekau daga jagaorantar kungiyar.

Yadda muka tattara alakluman

Kungiyar Boko Haram na daya daga cikin kungiyoyin da duniya ba ta fahimta ba.

Domin gane yadda kungiyar ke tafiyar da ayyukan ta'addancinta, BBC ta duba rahotannin kafafen yada labarai na cikin gida da na waje suka wallafa game da hare-haren 2016 da 2017, kuma mun yi la'akari da ainihin abubuwan da suka faru a lokacin kowane hari.

Amma dole ne a samar da daidaito tsakanin sakamakon wannan binciken da matsalar tara bayanai a yankin na Afirka ta yamma.

Andrew Walker dan jarida ne da ya dade yana yin rahotanni akan Najeriya, kuyma ya fada wa BBC cewa ba za a iya samun ainihin alkaluman ababen da suka faruba saboda yayanyin rikicin.

Amma ta hanyar duba rahotanni daga kafafen watsa labarai 48 daga harsunan Ingilishi, da Farnsanci, da Larabci da harsunan Kanuri da Hausa da Zarma a yankin Afirka ta yamma, wannan rahoton ya ba da haske ga yanayin munanan hare-haren da kungiyar ta ke kai wa.

Hare-hare na karuwa, amma wuraren da ake kai harin basu sauya ba

Boko Haram ta kai jimillar hare-hare 150 a 2017, inda aka sami karuwar hare-hare 127 idan aka kwatanta da wadanda ta kai a 2016.

A dukkan wadannan shekarun biyu, kungiyar ta kai mafi yawan hare-haren nata a watan Janairu ne, inda BBC ta gano cewa ana samun karuwar hare-haren ne bayn kalaman shugaba Buhari na cewa an gama da kungiyar.

Amma wuraren da kungiyar Boko haram din tafi kai hare-harenta basu sauya ba sosai a cikin wadannan shekarun biyu.

Najeriya ta fuskanci mafi yawan manyan hare-hare a cikin shekarun 2016 da 2017 ne, inda jihar Borno ta kasance wadda ta fi jin jiki.

Kungiyar ta kuma nuna ikonta na kai wasu hare-hare nesa ta inda aka zsaba gani, domin ta kai hari a yankin Arewa mai nisa na Kamaru da yankin Diffa na kasar Nijar da kuma yankin tafkin Chadi.

Wannan ya yi kama da jerin hare-haren shekarar 2016, amma akwai bambanci, domin Najeriy ata fuskanci karuwar hare-haren inda a Nijar lamarin yayi sauki.

Yanayin hare-haren

Boko Haram ta kai hare-hare 90, na kunar-bakin-wake kuma guda 59 a 2017.

Najeriya ce ta fuskanci mafi yawan hare-haren.

A tsallaken iyaka kuwa, kungiyar ta rika kai wa Kamaru harin kunar bakin wake ne fiye da na gaba gadi.

A shekarar 2016, kungiyar ta aiwatar da hare-haren da masu kama da wadannan.

Alkaluma sun bayyana karuwar kai hare-haren kunar bakin wake.

A Najeriya, kungiyar ta kara kai hare-haren kunar bakin waken daga 19 a 2016 zuwa 38 a 2017, inda Kamaru ma ta sami irin wannan karuwar hare-haren.

Harin kunar bakin wake shi ne yafi yawa a birnin Maiduguri na tarayyar Najeriya, inda birnin ya cigaba da zama cibiyar wannan ta'addancin.

Rashin rayuka bai sauya ba sosai

Akalla mutum 967 aka bada rahoton sun rasa rayukansu a hare-haren na Boko Haram a 2017, inda aka sami karuwar mace-mace idan aka kwatanta da 2016 inda aka sami mutum 910 da suka mutu.

Mafi yawan mace-mace a 2017 sun auku a Maiduguri ne, kuma an sami karuwar mutanen da ke szaune a birnin zuwa kimanin mutum miliyan biyu saboda masu neman mafaka daga hare-haren kungiyar Boko Haram.

A wasu sassa na najeriya kuwa, an sami karuwar mutuwar mutane a Magumeri, da Konduga da Damaturu da kuma Mubi.

Ba a sami sauye-sauye masu yawa ba a yadda Boko Haram ke kai hare-hare a shekaru biyun da suka gabata.

Mafi akasarin hare-haren da ta kai a shekarun 2016 da 2017 sun kasance a kan kauyuka ne da sojin kasashen.

Boko Haram ta cigaba da kai hari akan masallatai da cibiyoyin 'yan gudun hijira masu tserewa tashin hankalin.

Dangantakar Boko Haram da IS

Babu takamaiman bayani game da dangantakar Boko Haram da IS.

Hare-hare 13 ne cikin 151 da Boko Haram ta kai suka sami goyon bayan IS, wanda ke nuna cewa babu wata alaka mai karfi tsakanin kungiyoyin biyu.

Yana yiwuwa dalilan haka sun biyo bayan matsin lambar da IS ta ke fuskanta a Iraki da Siriya na da tasiri domin IS ta rasa daular ta ta kafa a can.

Me yasa aka kasa gama wa da Boko Haram?

A shafe shekaru masu sukar lamirin gwamnatocin Najeriya na tuhumarsu da kin ba rundunonin sojin kasar isassun makaman da suke bukata a fagen yaki da Boko Haram.

Amma da alama wannan zai sauya a 2018, bayan da Amurka ta yarda za ta sayar wa Najeriya makamai.

Amma kafin zuwa wannan lokacin, da alama Boko Haram na nan da sauran karfinta, inji Tomi Oladipo, wakilin tsaro na BBC.

Hakkin mallakar hoto AFP/GETTY IMAGES
Image caption Nigeria's military has struggled to defeat the Boko Haram threat

"Duk da cewa gwamnatin Najeriya ta sha fadin cewa ta ga bayan Boko Haram, amma bangarorin kungiyar sun ci gaba da janyo matsalolin tsaro a yankin arewa maso gabashin Najeriya da ma yankin tafkin Chadi," inji shi.

A ganin Oladipo, Boko Haram ta na dogaro da dabarun yakin sunkuru ne wajen cigaba da fuskantar hare-haren dakarun gwamnati.

Labarai masu alaka