Karancin suga ya janyo zanga-zanga a kasar Habasha

Karancin suga a Habasha, ya sa jama'a da dama dai na cin abubuwan da ake hadawa da sigan kamar cincin da kek Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Karancin suga a Habasha, ya sa jama'a da dama dai na cin abubuwan da ake hadawa da sugan kamar cincin da kek

Habasha na fuskantar matsanancin karancin sukari wanda ya haifar da zanga-zanga da mutuwar sama da mutum 10 zuwa yanzu.

Hukumar samar da sukari a kasar, ta dora alhakin wannan karanci a kan rashin kyawun yanayi wanda ya janyo raguwar sarrafa shi.

A yanzu gwamnati na cewa nan gaba kadan za ta karbi fiye da tan 200,000 na sukari daga Aljeriya da Thailand, don rage zafin wannan hali wanda hatta 'yan kasuwa ke ci gaba da iyakance sugan da za su sayar a shaguna da manyan kantunan kasar.

Wakilin BBC a kasar, ya ce ba a fiye samun sugan ba ma sai anje manyan kantuna, kuma talaka da kananan 'yan kasuwa ne suka fi jin jiki a wannan yanayi na karancin sugan da ake fama dashi a kasar.

Karancin sugan ya sanya farashinsa tashi inji wakilin na BBC.

Shin me ya sa muke san shan alawa?

Ko wayar salula na iya warkar da ciwon suga?

Wannan yanayi da ake ciki ya sa gwamnatin kasar bullo da wani shiri na kayyade sukarin da za a sayarwa duk wani magidanci a kasar a duk wata.

Wani mai shago a kasar, ya sahida wa BBC cewa, suna sayar wa magidanta sukari kilogram biyar a duk wata, kamar yadda gwamnatin kasar ta bayar da umarni.

Wata mata da wakilin na BBC ya tattauna da ita, ta ce saboda karancin sukarin da ake fama da shi a kasar, yanzu 'ya'yanta hudu sun dai na cin cincin da kek.

Labarai masu alaka