Gobara ta kashe mutum 37 a asibiti a Koriya Ta Kudu

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Yadda masu kashe gobara suka dinga fama da wutar

A kalla mutum 37 ne suka mutu, wasu 70 kuma suka jikkata a wata mummunar gobara da aka shafe kusan shekara 10 ba a yi irin ta ba a Koriya Ta Kudu.

Rahotanni sun ce gobarar ta faro ne daga dakin bayar da kulawar gaggawa na Asibitin Sejong da ke birnin Miryang a kudu maso gabahsin kasar.

Kusan marasa lafiya 200 ne suke cikin asibitin da kuma wasu da ke cibiyar kula da tsofaffi na asibitin a lokacin.

Wannan gobara dai ita ce mafi muni da aka yi a Koriya Ta Kudu cikin shakara 10 da suka gabata, kuma ana tsammanin yawan wadanda suka mutu zai karu, saboda yadda wadanda suka jikkata ke cikin halin ha'u'la'i.

Masu aikin kashe gobara sun ce yawancin wadanda suka mutun hayakin da suka shaka ne ya kashe su.

Daga cikin wadanda suka mutu har da wasu ma'aikatan asibitin uku da suka hada da wani likita da ma'aikaciyar jinya da mataimakiyarta.

Hukumomi sun bayar da mabambantan alkaluma na yawan wadanda suka mutu, inda da fari 'yan sanda suka ce mutum 41 ne suka mutu, amma ma'aikatan kashe gobara da majiyoyin asibiti sun ce mutum 37 ne suka mutu.

Birnin Miryang yana da nisan kilomita 270 daga babban birnin kasar Seoul.

Asibitin dai ya kware wajen bai wa tsofaffi kulawa da ma sauran marasa lafiya, in ji wata kafar watsa labarai ta intanet.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wannan gobara dai ita ce mafi muni da aka yi a Koriya Ta Kudu cikin shakara 10 da suka gabata
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Gobarar ta faro ne daga dakin bayar da kulawar gaggawa na Asibitin Sejong

ta kara da cewa wani majinyaci da ya tsira Jang Yeong-jae, ya ce yana hawa na biyu na benen asibitin sai ya jiwo ihun ma'aikatan jinya suna cewa wuta, wuta, don sanar da mutane halin da ake ciki.

'Iface-ifacen neman dauki'

"Amma da na bude kofa don guduwa sai na ga hayaki ya turnuke wajen."

Mista Jang ya ce sai ya bude taga ya sauka ta kan tsanin da masu kashe gobara suka ajiye.

Ya kara da cewa akwai tsofaffi da ba su da lafiya sosai a sauran hawan benayen.... Ina tababa idan har sun samu tsira."

Shugaban hukumar kashe gobara Choi Man-woo, ya ce har yanzu ba a san me ya jawo gobarar ba.

Kafofin watsa labarai sun ce ba bu abubuwan kashe gobara na gaggawa a baki daya ginin asibitin.

Mr Choi ya ce gobarar ta fara ne da misalin karfe 07:30 na sfaiyar kasar da ranar Alhamis, kuma an shafe sa'a uku an kashe ta.

An samu nasarar fitar da marasa lafiya 94 da ke kusa da ginin cibiyar kula da tsofaffin.

Shugaban kasar Koriya Ta Kudu dai ya yi wani taron gaggawa don tattauna yadda za a shawo kan gobara irin wannan nan gaba.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ba a san abun da ya jawo wutar ba
Hakkin mallakar hoto Reuters

Labarai masu alaka