Zuwan Kwankwaso Kano na da hadari —'Yan sanda

Kwankwaso da Ganduje Hakkin mallakar hoto KANO GOVERNMENT HOUSE
Image caption Masana harkokin siyasar Najeriya sun ce rikicin bangar da ake yi a Kano babban koma-baya ne da ka iya rage kimar jihar a idon sauran jihohin Najeriya kasar

Rundunar 'yan sandan jihar Kano da ke arewacin Najeriya, ta shawarci tsohon gwamnan jihar Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, da ya soke ziyarar da ya yi niyyar kai wa jihar a ranar talata 30 ga watan Janairu, saboda barazanar tashin hankalin da za a iya samu.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Rabi'u Yusuf ne ya bayyana hakan a wajen wani taron manema labarai da aka yi a birnin Kanon ranar Juma'a.

Mista Yusuf ya ce ya zama wajibi a shawarci Sanata Kwankwaso ya soke ziyarar tasa, duk kuwa da cewa yana da cikakkiyar dama da 'yancin walwala a matsayinsa na dan asalin jihar.

Ya kara da cewa rahotanni sun nuna cewa akwai matukar tsoro a zukatan al'ummar jihar na irin tashin hankalin da za a iya samu.

Sai dai kawo yanzu Sanata Kwankwaso bai ce komai ba game da matakin rundunar 'yan sandan.

"'Yan sanda sun samu bayanan da ke nuna cewa mutane suna fargabar wasu bata-garin 'yan siyasa za su iya fakewa da ziyarar tasa su yi abun da bai kamata ba na tashin hankali.

"Wannan ne ya sa ya zama dole hukuma ta dauki mataki na dakile duk wani abu da zai kawar da zaman lafiyar da ake da shi a jihar, in ji Kwamishina Rabi'u Yusuf.

An raba gari tsakanin Ganduje da mataimakinsa ne?

An hana Ganduje da Kwankwaso tarukan siyasa

Yadda Kwankwaso da Ganduje 'ke siyasar banga a Kano'

Ya kuma jaddada aniyar rundunar ta ci gaba da jajircewa da tsayawa tayin daka da yin adalci ga da bai wa ko wanne dan siyasa damar yin al'amuran siyasrsa ba atre da tsoro ko faragaba ko cin zarafi ba.

Tun da fari dai Sanata Kwankwaso ya shirya kai ziyara jiharsa ta Kano ne a ranar Talata 30 ga watan Janairu, inda rabonsa da kai ziyara tun lokacin da ya je yi wa Gwamna Abdullahi umar Ganduje ta'aziyar rasuwar mahaifiyarsa a watan Maris 2016.

Tun daga wannan ziyara ce kuma aka fara samun takun-saka tsakanin magoya bayansa da na Gwamnan Ganduje, wanda a baya kansu a hade yake.

Ko a lokacin bikin karamar sallar 2017 ma sai da aka yi fito-na-fito tsakanin magoyan bayan shugabannin biyu, inda har aka jikkata wasu da dama.