'Yan gudun hijirar Kamaru sama da 43,000 sun shiga Najeriya

Yawancin 'yan gudun hijirar mata ne da kuma kananan yara. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Yawancin 'yan gudun hijirar mata ne da kuma kananan yara.

Wasu alkaluma da hukumomin agaji suka bayar sun nuna cewa 'yan kasar Kamaru fiye da dubu arba'in da uku ne suka tsere zuwa Najeriya.

Tserewar ta biyo bayan dirar mikiyar da gwamnatin Kamarun ke yi wa 'yan a-ware na yankunan arewa maso yammaci da kudu maso yammaci, masu amfani da turancin Ingilishi a kasar ta Kamaru.

'Yan gudun hijirar, wadanda yawansu ke ci gaba da karuwa, sun fantsama jihohin Kuros Riba, da Binuwai,da Enugu da kuma Akwa Ibom.

Adadin 'yan gudun hijirar yanzu ya nunka kusan sau uku, bisa adadin da jami'an majalisar dinkin duniya da na Najeriya suka bayar makwanni biyu da suka gabata.

Daraktan hukumar agajin gaggawa na jihar Binuwai, Mista John Inaku ya shaida wa BBC cewa, "A yanzu haka kuma akwai 'yan gudun hijirar Kamaru fiye da dubu talatin da uku, wadanda suka sami mafaka a jihar Kuros Riba ta Najeriya, mai makwabtaka da yankin kudu maso yammacin Kamarun."

Shugaban bayar da agajin gaggawa na jihar Binuwai ya yi bayanin cewa,"Yawancin 'yan gudun hijirar mata ne da kuma kananan yara. Kuma wasu matan ma suna da tsohon ciki, wasu kuma tsofaffi."

Shugaban kwamitin kula da batutuwan 'yan gudun hijira na majalisar wakilai ta Najeriya, Honarabul Sani Zorro, ya kara da cewa,"Su wadannan 'yan gudun hijira a yanzu haka suna kauyuka da garuruwan da suke ciki suna nisan kilo mita daya zuwa biyu daga iyakarmu da Kamaru.

"Abin da yake faruwa shi ne jami'an tsaron Kamaru na yin kutse suna kama wasu daga cikinsu suna cewa 'yan ta'adda ne a tafi da su to an hana wannan, kuma yin irin wanann kutsen na jami'an tsaro zuwa wata kasar zai iya kawo takaddama har ayi yaki."

Masu lura da al'amura dai na ganin batun wadannan 'yan gudun hijira wani babban kalubale ne, ba wai ga kasar ta Kamaru ba, har ma ga makwabtanta da sauran yankin Afirka ta yamma.

Labarai masu alaka