Yadda Boka ya hana masu jinin al'ada zuwa makaranta

Yadda Boka ya hana masu jinin al'ada zuwa makaranta

Ana samun matsalolin kyara da tsangwama ga masu al'ada a fadin duniya. A wasu bangarorin Afirka, ana nuna wa mata masu jinin al'ada wariya saboda ana daukarsu marasa tsarki. Wannan ne halin da wasu 'yan mata dalibai ke ciki a yankin tsakiyar Ghana. An haramtawa 'yan mata masu jinin al'ada tsallaka kogin Ofin don zuwa makaranta, bisa dokar da wani boka da ake bauta wa a kogin ya bayar, hakan kuma yana shafar neman iliminsu.

A sakamakon haka, 'yan matan yankin suke samun koma baya a zangon karatunsu- Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa yarinya daya cikin goma ba ta samun zuwa makaranta a yankin saboda batun jinin al'ada.