Wainar da matan Hausawa ke toyawa a shafukan sada zumunta
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Wainar da matan Hausawa ke toyawa a shafukan sada zumunta?

Ku latsa alamar lasifikar da ke sama don sauraron cikakken shirin tare da Fatima Zahra Umar:

Adikon Zamani na wannan mako ya yi duba ne kan irin abun da ke jan hankalin mata a shafukan sada zumunta, kamar taimakon al'umma da tsegumi, da tallace-tallace, da cin zarafin juna da dai sauran su.

Amfani da shafukan sada zumunta na zamani (Social Media), a tsakanin matan al'ummar Hausawa ya yadu tamkar ruwan dare gama duniya.

A shirin Adikon Zamani na wannan makon za mu duba dalilan da yasa amfani da shafukan sada zumunta na zamani ke sa mata ke shagaltuwa.

Wasu na amfani da wadannan shafukan ne, musamman ma Facebook da Instagram domin tallafa wa al'umma da fadakar da mata a kan batutuwan da suke damunsu.

Misali akwai shafin Open Diaries a Instagram, wanda Fatima Fouad Hashim da wasu bayin Allah su ka bude domin taimakawa da shawarwari akan harkokin rayuwa na yau da kullum.

Sun kware sosai a harkar har suna shiga cikin al'umma su tallafa musu da kudaden da aka hado daga mabiya shafin.

Wasu kuma kamar Hajiya Aisha Falke mai wallaffa shafin Northern Hibiscus a Instagram, su na amfani da shafukansu domin kasuwanci da nishadantarwa.

Ta kan saka labarai masu kalar tsegumi da abun dariya da kuma tallace-tallacen kayan sayarwa irin jakukuna, atamfofi da sauransu.

Akwai wasu kuma wadanda suka shahara a harkar sayar da kayan mata domin taimakawa mata a fagen aure.

Suna tallan irin hade-hadensu da labaran matan da suka yi amfani da kayan kuma suka gamsu da hakan.

Wasu kuma nasu shafukan na ilmantarwa ne da karfafa wa mata gwiwa irin su shafin The Almajira da ke Instagram.

Amma kuma abun takaici shi ne, akwai wasu shafukan da mata ke kafawa domin gulma, zagi da cin mutuncin sauran 'yan uwa mata.

Abun takaicin shi ne mafi yawancin masu bin wadannan shafukan mata ne, kuma sai mutum ya ga suna jin dadin zagin da wulakanta matan da ake yi a wadannan shafukan.

Ni a ganina wannan ba abun da ya dace ba ne a al'adance ko a addinance. Ina fatan za mu gyara wannan yayi na bude shafukan sadarwa domin zage-zage da cin mutuncin wasu.