Jirgin ruwa ya bace dauke da mutane 50 a Kiribati

Kirikati
Image caption Jirgin ya taso ne daga Nonouti zuwa Betio

Masu aikin ceto na ci gaba da binciken wani karamin jirgin ruwa da ya bata a tsibirin Kiribati dauke da mutane 50.

Jirgin mai suna MV Butiraoi ya taso ne daga tsibirin Nanouti a ranar 18 ga watan Janairu, inda ake sa ran zai shafe kwanaki biyu a hanya.

Amma a daren Alhamis aka fara samun labarin ya bata, kuma jami'ai daga New Zealand da Fiji sun shiga aikin neman jirgin.

Jami'an ceto a New Zealand da ke taimakawa da aikin binciken, sun ce jirgin ya baro Nanouti ne da ke tsakanin kilomita 260 zuwa Betio, babbar tashar kasar.

New Zealand ta kuma aika da wani jirgin sojin sama domin aikin ceto jirgin da ya bata.

Babban jami'in da ke jagorantar binciken, John Ashby ya ce suna iya kokarinsu domin gano jirgin da kuma fasinjan da ke cikinsa.

Ya ce sun fahimci cewa ashe an yi gyaran daya daga cikin fankar jirgin kafin ya tashi, kuma a cewarsa wannan na iya kasancewar sanadin halin da jirgin ya shiga a yanzu.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption New Zealand ta tura wani jirgin sojin sama domin aikin ceto jirgin da ya bata.

Labarai masu alaka