Kabul: Harin bam ya kashe mutum 95 kana ya raunata 158

A wounded boy with blood on his face being bandaged by medical staff Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Akalla mutum 151 ne suka sami rauni a wannan harin

Akalla mutum 95 suka rasa rayukansu inda kuma 158 suka raunata a wani harin bam na kunar bakin wake da aka kai a tsakiyar birnin Kabul na Afghanistan, inji jami'ai.

Wadanda suka kai harin sun tuka wata motar daukar marasa lafiya ce da suka makare ta da bama-bamai, inda suka wuce wani wurin duba mutane da 'yan sanda suka kafa ba tare da an gane su ba.

Harin ya auku ne kusa da tsohon ginin ma'aikatar harkokin cikin gida, wanda ke kusa da ofisoshin Tarayyar Turai da Babbar Majalisar Zaman Lafiya.

Kungiyar Taliban ta dauki alhakin wannan harin.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Wannan shi ne hari na biyu a cikin mako guda

A makon jiya ma kungiyar ta Taliban ta kashe mutum 22 a wani katafaren otel da ke Kabul.

Wadanda suka gane wa idonsu al'amarin sun ce wurin - wanda cibiya ce ta ofisoshin jakadancin kasashen waje da shalkwatar 'yan sandan kasar - yana cike makil da jama'a a daidai lokacin da bam din ya fashe.

An rika gain hayaki a sassa daban-daban na birnin.

Hakkin mallakar hoto WAKIL KOHSAR
Image caption Asibitocin birnin Kabul na ta karbar wadanda harin ya rutsa da su
Hakkin mallakar hoto BBC Afghan
Image caption Ana iya hango hayaki daga inda harin ya auku a sassa babn-daban na birnin Kabulk

Labarai masu alaka