Ana binciken kamfani da cuwa-cuwar mabiya a shafin twitter

Twitter Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Ana bincike kan kamfanin Devumi a Amruka da laifin kirkirar jabun mabiya da ke bin fitattun mutane a shafukan sada zumunta

Hukumomi a New York sun kaddamar da bincike a kan wani kamfanin Amurka da ake zargi ya sayar da miliyoyin mabiya na jabu a shafukan sada zumunta.

An kaddamar da binciken ne kan kamfanin a ofishin alkalin alkalan New York.

Ana zargin Kamfanin mai suna Devumi da kirkirar jabun mabiya da ke bin fitattun mutane da 'yan siyasa da 'yan wasa da 'yan jarida ga wadanda ke neman suna a shafukan sada zumunta.

Wani bincike da New York Times ta gudanar ta gano akalla mabiya 55,000 da kamfanin ya sauya na jabu daga shafukan mutane na twitter.

A cikin wata sanarwa, kamfanin Twitter ya bayyana cewa wannan abu ne da ba zai amince da shi ba.

Sai dai kuma Kamfanin na Devumi ya musanta zargin yana sayar da mabiyan shafukan sada zumunta na jabu da kuma satar bayanan mutane na asali.

Labarai masu alaka