Tsibirin da kasashe biyu ke karba-karbar mallakarsa

Tsibirin Faisans Hakkin mallakar hoto Alamy
Image caption Ba mutumin da ke zaune a tsibirin na Faisans da ke iyakar Faransa da Spaniya a Kogin Bidasoa, wanda tsawonsa ya dan zarta mita 200 da fadin mita 40 kawai.

A mako mai zuwa ne Faransa za ta mika wani sashe na kasarta mai fadin murabba'in sama da kafa 32,000 ga kasar Spaniya ba tare da wani yaki ba. Amma kuma bayan wasu watanni shidan ita ma Spaniya za ta sake dawo wa da Faransar wannan yanki bisa radin kanta.

Kamar yadda Chris Bockman ya hada mana wannan rahoton haka kasahen biyu ke karba-karbar mallakar wannan yanki sama da shekara 350, wanda tsibiri ne da ke tsakanin kasashen biyu.

Wurin shakatawa na bakin teku na Hendaye shi ne gari na karshe da ke kan iyakar Faransa da Spaniya. A lokacin sanyi duk da tsananin huturu za ka ga gwanin ban sha'awa halittun ruwa sun baibaye rairayin bakin tekun.

Daga 'yar tazara kadan sai garin nan mai tarihi na Hondarribia na Spaniya, da kuma can gefe daya da makwabcinsa wato garin Irun.

Iyakar da ke tsakanin wadannan garuruwa ita ce ta kogin Bidasoa, wanda ruwansa ya raba kasashen na Turai biyu.

Idan ka yi tafiya daga bakin kogin, sai ka ga yanayinsa ya sauya. Kana tafiya sai ka ga gine-gine masu ban sha'awa har ka daina ganinsu sai kuma manyan gidajen ajiya na masana'antu a bangarin kasar ta Faransa, yayin da a bangaren kasar Spnaiya kuwa za ka ga dogayen gidajen jama'a.

Hakkin mallakar hoto Google
Image caption An fafata yaki tsakanin Faransa da Spaniya a kan mallakar tsibirin, wanda aka yi yarjejeniyar sulhu a shekarar 1659

To amma ni duka ba wadannan na zo na gani ba, abin da na yo takakakka dominsa shi ne tsibirin Faisans. Ba abu ne mai sauki ba gano wannan wuri, saboda kusan duk wanda na tambaya, ba wanda ya san dalilin da ya sa nake son zuwa can. Sai kawai su ce min, ''ba wani abin kallo a can, saboda ba wani mutum da ke zaune yake rayuwa a can, ba wani wurin yawon bude idanu ba ne kamar tsaunin Mont St Michel.''

Duk da haka shi wannan wuri yana nan yadda yake, tsibiri ne a tsakiyar kogi tsakanin wadannan kasashe biyu, shiru kake ji ba wata hayaniya a cikinsa, ga bishiyoyi da kuma ciyayye da aka gyara su da kyau, da kuma wani tsohon gini na tarihi inda aka yi wata yarjejeniyar sulhu ta tarihi a shekarar 1659.

Tsawon wata uku kasashen Spaniya da Faransa suka yi yarjejeniyar kawo karshen yakin da suka dade suna fafatawa tsakaninsu a kan tsibirin, inda a karshe aka ayyana shi a matsayin yankin da ba wanda zai mallake shi dindindin a tsakaninsu. An yi gadojin katako daga bangaren kasashen biyu zuwa cikin tsibirin, yayin da dakarun kowace kasa suka zauna cikin damara a lokacin da aka fara tattaunawar.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sarki Louis na 14 na Faransa da Sarki Philip na hudu na Spaniya sun gana a tsibirin na Faisans a 1660

A karshe dai an sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya wadda aka yi wa lakabi da yarjejeniyar Pyrenees. A bisa yarjejeniyar aka shata iyaka, sannan kuma aka tsara yin karba-karbar iko da yankin. An kammala yarjejeniyar ne da kulla auren saraki, tsakanin Sarkin Faransa Louis na 14 wanda ya auri 'yar Sarkin Spaniya Philippe na hudu.

just over 200m long and 40m wide.