Yadda aka sace wa wata kurma jaririnta a Kaduna

Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriya, Idris Kpotum ya kafa runduna ta samusamman kan dakile sace-sacen mutane Hakkin mallakar hoto Getty Images

An sace jaririn wata mata kurma wadda mijinta kurma ne bayan an yi wa matar tiyatar haihuwa a jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya.

Lamarin dai ya faru ne a asibitin dan tsoho da ke cikin birnin Kaduna.

Shugaban kungiyar guragu na jihar Kaduna, Rilwanu Muhammad Abdullahi, ya ce kungiyarsu na zargin wata mata wadda take haba-haba da kuramen a lokacin da aka kai ta asibiti da sace jaririn.

Da aka yi wa kurmar aiki sai aka bai wa mijin kurmar, wanda shi ma kurma ne, ya je ya sayo mata magani.

Ana ba shi takardar maganin da zai sayo din kuwa, sai shi mijin kurmar ya yanke jiki ya fadi.

Kuma da hankalin mutane ya koma kan mijin, sai wata mata wadda ta yi kamar tana taimaka wa kuramen ta tafi. Kuma daga nan aka nemi jaririn aka rasa.

Jami'in hulda da jama'a na rundunar 'yan sandan Kaduna, Aliyu Mukhtar, ya shaida da wa BBC cewar a iya binciken da rundunar ta yi, ma'aikatan asibitin ba su da laifi cikin lamarin satar jaririn.

Sai dai kuma, rundunar ta ce tana iya kokarinta wajen samun wannan matar wadda ta zo ta yi wa iyayen jaririn da aka sacen hidima domin gano inda yaron yake.

Sace-sacen mutane dai a jihar ta Kaduna an fi yi ne domin garkuwa da mutane da zummar neman kudin fansa.

Hakkin mallakar hoto NIGERIA POLICE
Image caption Sufeto Janar na 'yan sandan Najeriya, Idris Kpotum ya kafa runduna ta samusamman kan dakile sace-sacen mutane

Labarai masu alaka