Nigeria: Fursunoni 430 sun samu shiga jami'a

Prisoners Hakkin mallakar hoto Getty Images

An bai wa fursunoni 430 guraben karatun digiri daban-daban a jami'ar karatu daga gida ta Najeriya (NOUN) domin su inganta rayuwarsu.

An kuma sallami wasu fursunonin 951 bayan da wasu masu ruwa da tsaki kan gyara ga gidajen yari suka tallafa musu.

A cikinsu akwai fursunoni uku da suke dab da kammala karatun digirinsu na uku a wasu jami'o'in Najeriya.

An kyale fursunonin su ci gaba da karatun jami'a ne, a wani bangare na gyare-gyaren da gwamnatin Najeriya ke yi ga ayyukan shari'a, musamman ma na inganta rayuwar fursunoni.

Kakakin hukumar kula da gidajen yari ta najeriya Mista Francis Enebore ne ya bayyana wannan a Abuja yayin da ya ke tattaunawa da manema labarai.

Ya kuma sanar da wani taro da babban daraktan hukumar gyara ga gidajen yari na kasa, Dr. Uju Agomoh ya halarta cewa an sallami fursunoni 951 bayan da suka cika dukkan ka'idojin da aka gindaya masu.

Labarai masu alaka