'Abin da ya sa aka zabi Buhari jagoran yaki da rashawa na Afirka'

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya na jawabi a taron AU
Image caption Buhari ya ce cin hanci babbar barazana ne ga tsaron kasa da hadin kanta da kuma rayuwar kasashen Afirka da al'ummarta

Gaba dayan nahiyar Afirka na kallon kyawawan matakan da Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ke dauka na yaki da cin hanci da rashawa, kuma kasashen nahiyar na son su yi koyi da kasar a wannan fanni.

Babban mataimaki na musamman ga shugaban na Najeriya a kan harkokin watsa labarai, Mallam Garba Shehu shi ne ya bayyana haka da cewa wannan ne dalilin da ya sa kungiyar tarayyar Afirka, AU, ta nada shugaban a matsayin jagoran yaki da cin hanci da rashawa na Afirka.

A ranar Litinin din nan ne a wurin taron shugabannin kungiyar a birnin Addis Ababa na Habasha, inda hedikwatar kungiyar take, Shugaban na Najeriya ya kaddamar da shirin yaki da cin hanci da rashawa na Afirka.

Daman tun a ranar Juma'a bayan da Buhari ya je taron na shugabannin kungiyar ta AU karo na 30, kakakin nasa a yayin wani taron manema labarai ya bayyana cewa Shugaban zai kaddamar da shirin tare da bude tambarin shirin yaki da rashawar na Afirka.

Mallam Garba Shehu ya ce, Shugaba Buhari ya shirya sosai domin taron na shugabannin Afirka na wannan karon wanda ke karewa ranar Litinin din nan, wanda aka yi wa take da sunan,'' Nasara a Yaki da Cin Hanci da Rashawa: Hanya mai Dorewa ga Bunkasar Afirka.''

"Kasancewar nahiyar ta ga cewa samun nasara a yaki da cin hanci da rashawa shi ne zai kai ta ga samun kyakkyawan sauyin da zai kai ta ga cigaba, kuma ganin cewa kusan babban abin da Shugaba Buhari ya sa a gaba kenan wanda kuma yake samun gagarumar nasara, shi ya sa kungiyar ta Afirka ta ga abin ya zo daidai da manufarta."

"Wannan ne ya sa kungiyar ta ba Shugaban na Najeriya ya cancanci ya jagoranci manufar tata, in ji Garba Shehu.

A yayin jawabin da Shugaba Buhari ya gabatar ga taron shugabannin Afirkar, bayan ba shi matsayin na jagoran shirin yaki da cin hanci da rashawar, ya yi alkawarin yin iya bakin kokarinsa domin ganin shirin kungiyar ta AU ya samu nasara da yin tasiri a shekara ta 2018 da ma bayanta.