An yi wa jaririya 'yar wata takwas fyade a India

There is growing anger in India against rape and sexual violence Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption There is growing anger in India against rape and sexual violence

An yi wa wata jaririya 'yar wata takwas fyade a Delhi babban birnin Indiya, inda ake zargin wani dan uwanta, abokin wasanta ne ya yi mata.

Rahotanni sun ce a yanzu haka yarinyar tana cikin mawuyacin halin a asibitin da aka kai ta bayan da ta samu munanan raunuka a ranar Lahadi.

'Yan sanda sun shaida wa manema labarai cewa sun kama matashin da ake zargi da aikata laifin mai shekara 28.

Kwamishinar kula da al'amuran mata ta Delhi wati Maliwal, wacce ta ziyarci jaririyar a asibiti ranar Litinin da daddare, ta bayyana irin raunukan da ta gani a jikin yarinyar da cewa abun tsoro ne matuka.

Al'amarin ya faru ne a ranar Lahadi, amma sai a ranar Litinin ne kafofin yada labarai suka samu labarin.

Ms Maliwal ta aika da sakon Twitter cewa, sai da aka yi wa yarinyar tiyata ta tsawon sa'a uku.

Yadda fyade da kisan 'yar shekara 6 ya harzuka India

Mata ta gantsara wa mai fyade cizo a mazakuta

India: Kotu ta yarda a zubar da cikin 'yar shekara 13 da aka yi wa fyade

Ta kara da cewa: "Kukan da jaririyar ke yi mai tsinka zuciya ya karade daukacin wajen kula da marasa lafiya na musamman na asibitin.

"Ta smau munanan raunuka ta ciki da wajen jikinta."


Sharhi daga Geeta Pandey, BBC News, Delhi

Irin wannan lamari mai muni na cin zarafin yara ya girgiza Indiya, kuma irin raunukan da jaririyar ta ji sun bai wa mutane da dama tsoro da har wasu ke tunanin ko an zo wani zamani ne da mutane ke abu tamkar dabbobi.

Sai dai wani kiyasi da gwamnati ta fitar ya nuna cewa ba a faye samun irin wannan mugun laifi ba.

Sai dai abun damuwar shi ne yadda a baya-bayan nan haka ke dan karuwa.

Wata kididdiga daga hukumar tattara bayanan laifuka ta kasa ya nuna cewa a shekarar 2016, an samu laifukan yi wa yara kanana fyade da aka yi rijistarsu har sau 19,765 a Indiya - abun da ya karu da kashi 82 cikin 100 daga 2015, inda a lokacin aka samu laifuka 10,854.

Shekaru biyu da suka gabata ma wani mutum ya sace jaririyar makwabciyarsa 'yar wata 11, yayin da take bacci a gaban mahaifiyarta, ya kuma shafe sa'a biyu yana mata fyade.

Sannan kuma a watan Nuwambar 2015, an sake sace wata jaririyar aka kuma ci zarafinta ta hanyar yi mata fyade a birnin Hyderabad na kasar Indiya.


Ms Maliwal ta sake wallafa wani sakon Twitter tana bayyana bakin cikinta.

"Me za mu yi? Ta ya ya za a iya bacci a Delhi a yau bayan da aka yi wa jaririya 'yar wata takwas fyade.

"Yanzu rashin tausayinmu har ya kai haka, ko kuwa kawai mun karbi hakan ne a matsayin kaddara?"

Ta kuma wallafa wani sakon inda take rokon Firai Minista Narendra Modi da cewa "ana bukatar a tsaurara dokoki a kuma kara samar da karin 'yan sanda don kare yara mata da ke kasar."

An ci gaba da samun karuwar fyade a Indiya ne tun bayan da wasu gungun mutane suka yi wa wata daliba mai shekara 23 fyade a motar bas cikin shekarar 2012 a Delhi babban birnin kasar.

Wannan al'amari ya jawo an shafe kwanaki ana zanga-zanga, aka kuma tursasawa gwamnati samar da wasu dokoki masu tsaurari dangane da fyade, da suka hada da kashe duk wanda aka kama da laifin.

Sai dai hakan bai hana ci gaba da samun karuwar yi wa mata da kananan yara fyade ba a fadin kasar.