Akwai 'yan mata 21m da 'ba a bukatarsu' a India

women with newborn babies in a maternity ward Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Mawallafa rahoton sun ce ya kamata Indiya ta sake duba halayyar fifita 'ya'ya maza kan mata

Bukatar da iyaye ke da ita ta samun 'ya'ya maza a Indiya a maimakon 'ya'ya mata ya janyo yanayin cewa akwai wasu 'yan mata miliyan 21 da ba a so a haifesu ba, inji wani rahoton gwamnatin kasar.

Rahoton da ma'aikatar kudade ta wallafa ya nuna cewa iyalai da dama na rika haihuwar 'ya'ya a jere har sai sun sami da namiji.

Mawallafan rahoton sun kuma ce wannan wani tsari ne na zabar irin jinsin da aka fi so maimakon zubar da ciki, amma sun yi gargadin cewa matakin ka iya rage yawan kayan more rayuwa ga 'yan mata.

Sun kuma ce, "Fifiko ga samun da namiji abu ne da ya kamata al'ummar Indiya ta sake dubawa".

Mawallafa rahoton sun gano cewa mata miliyan 63 "sun bace" daga cikin jumillar alkaluman mutanen Indiya.

Sun ce wannan halayyar ta sa ana zubar da cikin 'ya'ya mata, kuma an fi bai wa 'ya'ya maza kulawa.

Gwaje-gwaje domin zabar jinsin 'ya'ya laifi ne a Indiya, amma duk da haka ana gudanar da su.

Wasu daga cikin dalilan da aka fi son 'ya'ya maza sun hada da:

  • Gado - maza ne kawai ke gadon iyayensu ba mata ba
  • Bukatar iyayen mata su biya sadaki domin aurad da 'ya'yansu mata
  • Mata na komawa gidan mijin da suka aura bayan aure

Wannan halayyar ta fifita 'ya'ya maza kan mata ya sa wata jarida ta wallafa wasu dalilai da ba su da tushe a kimiyya, don a sami haihuwar 'ya'ya maza, inda ta ke ba da shawarar a rika fuskantar yamma a yayin da ake barci, da kuma yin jima'i a wasu ranaku na mako.

Jihohin da wannan lamarin ya fi shafa su ne Punjab da Haryana, inda jihar Meghalaya ce wadda lamarin bai shafa ba sosai.

A jihohin Punjab da Haryana, akwai yara maza da shekarunsu basu wuce bakwai ba ga 'yan mata 1,000 idan aka kwatanta shekarunsu, in ji mawallafan rahoton.

Labarai masu alaka