Odinga ya rantsar da kansa a matsayin shugaban Kenya

Raila Odinga

An rantsar da madugun 'yan adawa a Kenya, Raila Odinga a matsayin 'shugaban kasa na jama'a' - duk da gargadin da gwamnatin kasar ta yi na cewa matakin - cin amanar kasa ne.

Mista Odinga ya yi rantsuwar dauke da koren baibul a gaban dubban magoya bayansa da suka taru a dandalin Uhuru Park da ke Nairobi, babban birnin Kenya.

Mista Odinga ya sha kaye a hannun Shugaba Uhuru Kenyatta a zaben shugaban kasa da aka gudanar a karshen shekarar da ta gabata.

Amma shi da magoya bayansu sun yi imanin cewa shi ne ya lashe zaben.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Magoya bayansa sun taru domin shaida rantsar da madugun 'yan adawa Raila Odinga a matsayin "shugaban kasa"

Daruruwan mutane sun taru domin kallon bikin, amma wasu mazauna birnin Nairobi sun zabi su ki fita zuwa wajen aiki domin suna tsoron barkewar tashin hankali.

Shugaba Uhuru Kenyatta ya fada wa kafofin watsa labarai da kada su nuna bikin, inda har aka rufe wasu tashoshin talabijin.

Mista Odinga ya ce haramcin da aka sanyawa kafafen watsa labaran ya nuna cewa mun bi sahun kasar Uganda, wacce ta hana watsa zabukan da aka gudanar a kasar a 2016.

Kazalika Shugaba Kenyatta ya zargi Mista Odinga da cin amanar kasa.

Sai dai cacar-bakan da aka yi tsakanin su bai hana tururuwar mutane zuwa dandalin Uhuru don shan rantsuwar mulkin Mista Odingan ba.

Image caption Magoya bayan Raila Odinga na gamayyar jam'iyyun siyasa na NASA suna fareti a cikin shirye-shiryensu na rantsar da shi a matsayin shugaban kasa a Nairobi

Labarai masu alaka