Kalli hotunan abubuwan ban al'ajabin da suka faru a duniya a makon jiya 20 - 26 Janairu

Zababbun hotuna da muka samo daga sassa daban-daban na duniya da aka dauka a makon jiya.

An aerial view shows a car driving along a bank of the Yenisei River, outside Krasnoyarsk, Russia, 25 January 2018. Hakkin mallakar hoto Ilya Naymushin/REUTERS
Image caption Hoto daga sama na nuna wata mota tana tafiya a gabar kogin Yenisei, a wajen birnin Krasnoyarsk na kasar Rasha, inda sanyi ya kai kasa da celsius 30.
A view of Mount Mayon volcano. as it erupted, from Our Lady of the Gate Parish church in Daraga, Albay province, south of Manila, Philippines, 25 January 2018. Hakkin mallakar hoto Romeo Ranoco/REUTERS
Image caption Dutse mai amon wuta na Mount Mayon ke amon wuta a kasar Philippines, inda ya sa mutum 40,000 suka yi kaura daga muhallansu.
Britain's Duchess of Cambridge, speaks to a patient during a visit to the sensory room of the Mother and Baby Unit at the Bethlem Royal Hospital in south London, Britain, 24 January 2018. Hakkin mallakar hoto Hannah McKay/REUTERS
Image caption 'Yar gidan sarautar Ingila, Catherine ta Cambridge ta ziyarci asibitin Bethlem Royal dake kudancin birnin Landan. Catherine na dauke da cikin dan ta na uku, wanda zai zama na uku a masu jiran gadon sarautar Ingila bayan Yarima Charles da Yarima William da Prince George da kuma 'yar gidan sarauta Charlotte.
Bangladeshi Muslim devotees return home on an overcrowded train after attending the Akheri Munajat in Dhaka, Bangladesh, 21 January 2017. Hakkin mallakar hoto ABIR ABDULLAH/EPA
Image caption Musulmi 'yan kasar Bangladesh na komawa gida bayan sun kammala sallah a rana ta uku da ake gudanar da ibadar Biswa Ijtema a birnin Dhaka babban birnin kasar. Wannan ne taro na biyu a yawan jama'a bayan na aikin Hajji.
Cloned monkeys Zhong Zhong and Hua Hua are seen at the non-human primate facility at the Chinese Academy of Sciences in Shanghai, China,, on 20 January 2018. Hakkin mallakar hoto China Daily via REUTERS
Image caption Birrai biyu da masana kimiyya suka samar ta hanyar hada 'ya'yan halitta a wani dakin bincike. An haifi birran ne masu suna Zhong Zhong da Hua Hua a wani dakin bincike a kasar Sin.
Orla Dean, 5, holds a placard during the Time's Up rally at Richmond Terrace, opposite Downing Street on 21 January 2018 in London, England. Hakkin mallakar hoto Chris J Ratcliffe/Getty Images
Image caption Mutane sun taru a daura da titin Downing a ranar farko ta tunawa da macin da mata suka yi a birnin Landan.
Revellers in costumes take part in the traditional "Correfoc" festival in Palma de Mallorca on 21 January 2018. Hakkin mallakar hoto JAIME REINA/afp
Image caption Bikin na Carrofec ana yin sa ne cikin dare, kuma 'yan bikin na shigar dodanni ne inda suke yin fareti a titunan garin suna wasan wuta.
Italy's Federica Brignone competes during the FIS Alpine World Cup Women's Giant Slalom on 23 January 2018 in Kronplatz, Plan de Corones, Italian Alps. Germany's Viktoria Rebensburg won the race ahead of Norway's Ragnhild Mowinckel, and Italy's Federica Brignone. Hakkin mallakar hoto TIZIANA FABI/AFP
Image caption Federica Brignone ta kasar Italiya na faftawa a gasar duniya ta kankara a bisa duwatsun Alps na Italiya. Viktoria Rebensburg ta Jamus ce ta yi na daya, kuma 'yar Norway Ragnhild Mowinckel ce tayi na biyu. Brignone ce ta uku.
A portrait of Robert Burns is projected on to the front of Prestonfield House in Edinburgh on Burns Night, 25 January 2018 Hakkin mallakar hoto Jane Barlow/PA
Image caption Ga hoton Robert Burns da aka haska a gaban gidan Prestonfield a birnin Edinburgh domin tunawa da rayuwar Burns din. Ana bikin tunawa da Burns a kowace ranar 25 ga watan Janairu musamman rubutattun wakokinsa da shan giyar Whisky.
A starling murmuration near the southern Israeli city of Rahat, in the Negev desert. Hakkin mallakar hoto MENAHEM KAHANA/afp
Image caption Wannan hoton tarin tsuntsaye an dauke shi ne a kusa da birnin Rahat na kasar Isra'ila a yankin hamadar Negev. Wannan abin burgewan na faruwa ne a lokacin da dubban tsuntsaye suke shawage a daidai faduwar rana.

Dukkan hotunan mallakin masu su ne.