Tsoro ne ya hana Kwankwaso zuwa Kano - Gwamnatin Kano

Gwamnan jihar kano Dr Abdullahi Umar Ganduje Hakkin mallakar hoto Facebook/Kano State Govt
Image caption Ganduje ya kasance abokin tafiyar Kwankwaso a baya, amma yanzu ba sa ga-maciji

Gwamnatin jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta yi watsi da hanzarin da tsohon gwamnan jihar Injiniya Rabi`u Musa Kwankwaso ya gabatar, cewa magabata ne suka shawo kansa har ya janye aniyarsa ta ziyartar Kanon.

A ranar Talata ne aka tsara Kwankwaso zai kai ziyarar don halartar wani gangami, ziyarar da ta zo daidai da wani taron bangaren gwamnatin Jihar ta Dakta Abdullahi Umar Ganduje, wanda ba sa ga-maciji da juna, lamarin da ya jefa al`umma cikin fargabar barkewar yamutsi.

A hirarsa da BBC kwsamishinan watsa labaran jihar, Mallam Mohammed Garba ya sheda wa wakilinmu Ibrahim Isa cewa barazana ta fi yawa a cikin al`amarin Sanata Kwankwaso, don haka bai yi mamakin soke ziyarar tasa ba:

Latsa alamar lasifika da ke kasa domin sauraron hirar

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Kwamishinan watsa labaran jihar Kano Mohammed Garba

Labarai masu alaka