Saudiyya ta kwato dala biliyan 106

An tsare mutanen ne a otel din Ritz Carlton da ke Riyadh Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An tsare mutanen ne a otel din Ritz Carlton da ke Riyadh

Antoni janarar na kasar Saudiyya ya ce gwamnati ta kwato kudi fiye da dala biliyan 106 karkashin shirinta na yaki da cin hanci da rashawa.

Sheik Saud al mojeb ya ce daga cikin mutum 381 da aka kira a watan Nuwamban daya gabata domin an yi mu su tambayoyi, har yanzu ana tsare da 56 daga cikinsu.

Ya ce an wanke sauran daga aikata laifi ya yinda an saki wasu ne bayan da suka amsa aikata laifi tare da mika kadarorinsu da kudi ga gwamnati.

Sai dai Sheik Mojeb be bayanna sunnayen wadanda ake zargi ba , sai dai rahotanni sun ce a cikinsu akwai yarimomi da ministoci da kuma yan kasuwa.

A kwanakin baya bayanan ne aka sako hamshakin dan kasuwanan yerima Alwaleed bin Talal da kuma Alwalid al Ibrahim, wanda ya malaki kafar watsa shirye shirye ta MBC daga otel din Ritz-Carlton da ke garin Riyadh.

Sai dai mutanen biyu sun musanta zargin da ake yi mu su amma kuma wasu majiyoyi na gwamnatin Saudiyyar sun ce mutunen sun yada su bada wasu kudade bayan da suka amince da aikata laifi.

Aika wannan shafi Facebook Aika wannan shafi Twitter Aika wannan shafi Messenger Aika wannan shafi Email Aika

Sauran da ake tsamanin cewa an sakosu sun hada da yerima Mitleb bin Abdullah wanda da ne ga mariyagi sarki Abdullah wanda majiyoyin suka ce ya mika kadarori da aka yi kiyasin cewa adadinsu ya wuce dala biliyan daya da kuma Ibrahim al Assaf wanda minitsa ne wanda kuma rahotani suka ce ba a same shi da laifi ba.

Sai dai Sheik Mojen ya ce ya ki cimma masalaha da sauran mutane 56 da ake tsare da su saboda binciken da ake cigaba da yi akansu game da zargin cin haci da rashawa.

Ana dai tsamammin cewa an wuce da su zuwa wani gadan yari daga otel din Ritz Carlton da ake tsare da su wanda zaa sake bude wa a watan gobe. A makon daya gabata ne dai ministan kudi na kasar Mohammed al Jadaan ya ce za a yi amfani da kudaden da aka kwato a wani shiri da aka ware ma kudi dala biliyan 13 domin tallafawa yan saudiyya samun saukin tsaddar rayuwar.

Sai dai wasu masana sun soki shirin yaki da cin hanci da rashawa na Yerima mai jiran gado Mohammen bil Salman mai shekara 32 wanda da ne ga sarki Salman, inda suka bayana shi a matsayin wani shiri na neman iko.

Ko daya ke yerima Mohammed din ya ce da dama daga cikin wadanda ake tsare sun yi ma sa muba'ya'a tun bayan da aka nada shi yerima mai jiran gado a watan yunin daya gabata.