Ko kifi zai iya maye gurbin nama?

Kifi na neman yafi nama saukin samu da saukin farashi a Najeriya Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kifi na neman yafi nama saukin samu da saukin farashi a Najeriya

A yayin da fulani makiyaya ke fuskantar matsaloli, masu su da kuma kiwon kifi a Najeriya, na ganin da sannu a hankali kifi zai iya maye gurbin nama a kasuwanni da ma gidaje.

Alhaji Sani Usman Rilwanu, shi ne shugaban kungiyar masu kiwon kifi a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya, ya shaida wa BBC cewa, a yanzu mutane da dama sun shiga harkar kiwon kifi.

Don haka kifi ke wadata sosai fiye da nama.

Ya ce, wani abu kuma da ya ke gani zai sa kifi ya fi nama wadata a ko ina, shi ne kifi daya zai iya kyankyashe dubu biyar ko ma fiye da haka, amma dabba ita haihuwarta ba ta wuce daya ko biyu sai lokaci-lokaci ake samun wacce zata haifi uku.

Don haka bisa la'akari da yawan kifin da ake kyankyashewa da kuma yadda a yanzu dabbobi ma ke nema su yi wuya, kifi ya maye gurbin nama, domin yafi nama saukin samu da saukin farashi.

Shi ma wani mai sayar da kifin a Kadunan, yace "A yanzu ko ba nama, su masu sayar da kifi zasu rike masu cin naman da kifi saboda wadatarsa".

Kiwon kifi dai a yanzu na samar wa da matasa da dama aikin yi a jihohin Najeriya.

Labarai masu alaka