Rundunar sojin Nigeria na gina titi a dajin Sambisa

Gina titi a Sambisa Hakkin mallakar hoto Nigerian Army

Rundunar sojin Najeriya ta fara wani aikin gina titi a tsakiyar dajin Sambisa da garuruwan da ke makwabtaka da shi a jihar Borno a arewa maso gabashin kasar.

A wata sanarwa da ta fitar, rundunar ta ce ta fara wannan aiki ne a kokarin ta na mayar da dajin wajen da mutane za su iya zama da kuma dandalin da sojoji za su dinga atisaye.

Wannan aiki wani bangare ne na ci gaba da kakkabe duk wani abu da bai dace ba a dajin na Sambisa, kamar yadda sanarwar ta ce.

Tuni dai an fara wannan aiki ta hanyar sare daji a hanyar garuruwan Gwoza da Yamteke da Bitta.

Kazalika an kuma fara aikin shimfida titi a hanyar Gwoza da Yamteke da Bitta da Tokumbere, wanda zai mike har zuwa cikin dajin Sambisa.

Dajin dai shi ne babbar mattatarar mayakan Boko Haram tsawon shekaru, kuma an yi imanin anan ne shugabannin kungiyar ke boye.

Sai ku latsa alamar lasifikar da ke kasa don sauraron karin bayanin Kakakin rundunar Burgediya Janar Sani Usman Kukasheka ya yi wa Haruna Shehu Tangaza:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Jawabin Kuka-Sheka a kan hanyar da ake yi a Sambisa
Hakkin mallakar hoto Nigerian Army
Hakkin mallakar hoto Nigerian Amry
Hakkin mallakar hoto Nigerian Army

Labarai masu alaka