Dan Nigeria ya sayi motar Arnold Schwarzenegger

An dai sayar da motar Mr Schwarzenegger a kan dala miliyan 2.5 Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An dai sayar da motar Mr Schwarzenegger a kan dala miliyan 2.5

Wani dan Najeriya, ya sayi motar shahararen jarumin fina finan Hollywood din nan Arnold Schwarzenegger, a cewar jaridar Punch ta kasar Nigeria.

Obi Okeke, da aka fi sani da Dr Bugatti, ya sayi motar Mr Schwarzenegger kirar Bugatti Veyron a kan kudi dala miliyan biyu da dubu dari biyar.

A cewar jaridar Mr Okeke wanda dilalin motocin Bugatti ne, ya ce yana da anniyar sayar da motar.

Mr Okeke dai, na da da kwastomomi sosai masu hannu da shuni , ciki har da dan wasan dambe Floyd Mayweather.

Wata jaridar wasanni ta kasar Spaniya da ake kira Top Gear, ta wallafa labarin Mr Okeke, inda ta yi masa lakabi da mutumin da ke iya sayar da motocci 93 a lokaci guda.